Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ban taɓa ganin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ƙyaƙyata dariya ba, har inga ƙarshen ganɗarsa ba, kawai ya kasance yana murmushi

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنين رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، قَالَتْ: مَا رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مُسْتَجْمِعًا قَطُّ ضَاحِكًا، حَتَّى أَرَى مِنْهُ لَهَوَاتِهِ، إِنَّمَا كَانَ يَتَبَسَّمُ.
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Ban taɓa ganin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ƙyaƙyata dariya ba, har inga ƙarshen ganɗarsa ba, kawai ya kasance yana murmushi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai zama mai kai matuƙa a dariya ba har aga ganɗarsa ta sama ba, ita ce naman dake rataye a saman maƙogwaro, kawai ya kasance yana murmushi ne.

Fa’idoji
  1. Dariyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance murmushi ce idan ya yarda da wani abu ko aka ƙayatar da shi da wani abu.
  2. Ibnu Hajar ya ce: Ban taɓa ganinsa ba yana ƙyaƙyata dariya ba ta inda zai tayin dariya cikakkiyar dariya mai fuskantowa da gabadayansa akan dariya ba.
  3. Yawaita dariya da ɗaga murya da ƙyaƙyata dariya bai zama daga siffofin mutanen kirki ba.
  4. Yawaita dariya yana tafiyar da kwarjinin mutum da kuma nutsuwarsa a tsakanin 'yan uwansa.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 24) (6092). صحيح مسلم (2/ 616) (899).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
DARIYARSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com