Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa lokacin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, ya cewa (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -: Ka tafi zuwa ga Aljanna ka duba ta, sai ya tafi ya kallace ta sosai sannan ya dawo, Sai (Malaika) Jibril ya ce: Eh, ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa ba wanda zai ji labarin ta da kuma abinda ke cikinta na ni'ima da girmamawa da alkarai sai ya so ya shigeta, kuma ya yi aiki saboda ita. Sannan Allah Ya kewaye Aljanna da abubuwan ki da wahalhalu na aikata umarni da kuma nisantar abubuwan da aka hana; to ya wajaba ga wanda yake son shigarta da ya ketare wadananan abubuwan kin. Sannan Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Ya Jibril! ka tafi ka duba Aljanna, bayan ya kewayeta da abubuwan ki, Sai ya tafi ya dubata, sannan ya zo sai ya ce: Eh, ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa ina jin tsoro da kada wani ya kasa shigarta saboda wahalhalu da tsananin da suke akan hanyarta. Lokacin da Allah Ya halicci wuta, sai ya ce; Ya Jibri! ka tafi ka kallaceta, sai ya tafi ya kallaceta. Sannan ya zo sai (Malaika) Jibril ya ce: Eh ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa babu wani da zai ji labarin azabarta da tashin hankalin cikinta, sai ya ki shigarta ya nisanta daga sabubban shigarta. Sannan Allah - mai girma da daukaka - Ya kewaye wuta, Ya sanya hanya zuwa gareta da sha'awowi da abubuwan jin dadi, sannan Ya ce: Ya Jibril, ka tafi ka yi duba zuwa gareta, Sai (Malaika) Jibril ya tafi sai ya yi duba zuwa gareta, sannan ya dawo sai ya ce: Ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoro na ji tausayin kada wani ya kasa tsira daga gareta; saboda abinda ke gefanta na sha'awowi da abubuwan jin dadi.
- Imani da cewa Aljanna da wuta suna nan a yanzu haka.
- Wajabcin yin imani da abinda ke boye da kuma dukkanin abinda ya zo daga Allah da manzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Muhimmancin hakuri akan abubuwan ki; domin su ne hanya masu kaiwa zuwa ga Aljanna.
- Muhimmancin nisantar abubuwan da aka haramta; domin su ne hanya mai kaiwa zuwa ga wuta.
- Sanya Aljanna abar kewayewa da abubuwan ki, wuta kuma da sha'awowi, shi ne ke hukunta jarraba a rayuwar duniya.
- Hanyar Aljanna mai wahala ce, kuma tana bukatuwa zuwa ga hakuri da fama tare da imani, hanyar wuta kuma abin cikawa ce da abubuwan jin dadi da sha'awowwi a anan duniya.
سنن أبي داود (7/ 122) (4744)، سنن الترمذي (4/ 319) (2560)، سنن النسائي (7/ 3) (3763)، شرح سنن أبي داود للعباد (537/ 15)، حاشية السندي على سنن النسائي (7/ 3).)، فتح الباري (18/317)، ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (30/276).