Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Jurisprudence for Muslim Women

Hadisai 1

Kada ku hana bayin Allah mata (zuwa) masallatan Allah, saidai su fita alhali ba su yi mummunar shiga ba

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا تَمْنَعُوا إِمَاءَ اللَّهِ مَسَاجِدَ اللَّهِ، وَلَكِنْ لِيَخْرُجْنَ وَهُنَّ تَفِلَاتٌ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Kada ku hana bayin Allah mata (zuwa) masallatan Allah, saidai su fita alhali ba su yi mummunar shiga ba».
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana majiɓincin al'amarin mace da wanda ke kula da ita game da hana mata zuwa masallatai, kuma ya umarci mata in zasu fita su fita ba tare da sun shafa tirare ba, kuma ba tare da sun yi mummunar shiga ba; dan kar su zama sababi a fitinar maza.

Fa’idoji
  1. Yin izini ga mace da yin sallah a masallaci idan an amincewa fitinuwa, kuma ta fita ba tare da ado ba, ba kuma tare da ta shafa tirare ba.
  2. An kafa hujja da shi akan cewa mace kada ta fita daga gidan mijinta sai da izininsa, dan fuskantar da umarnin izinin zuwa ga mazajen.
  3. Kwaɗayin Musulunci game da mata, da rashin hana su abin da zai iya zama alheri a cikinsa na fita dan neman ilimi da kuma waninsa.
  4. Tabbabatar da shugabancin namiji akan mace da kuma kulawarsa gareta.
Madogara

سنن أبي داود (1/ 423) (565). شرح سنن أبي داود للعباد (78/ 6). شرح أبي داود للعيني (3/ 50). النهاية في غريب الحديث والأثر ص(109).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com