Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa

عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ لِي عَنْ أُمَّتِي الخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ».
Daga ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa».
Ibnu Majah da Baihaki da wasun su ne suka ruwaito shiDarajaNawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Lallai Allah Ya yi wa al'ummarsa rangwame akan halaye uku: Na farko: Kuskure, shi ne abin da ya bijiro daga garesu ba tare da ganganci ba, kuma shi ne musulmi ya nufi wani abu da aikinsa sai aikin na sa ya dace da abin da bai yi nufi ba. Na biyu: Mantuwa, shi ne musulmi ya zama mai tina wani abu, saidai a lokacin aikata shi sai ya manta shi, to babu zunubi a kan hakan. Na uku: Tilastawa, za’a iya tilastawa bawa yin wani aikin da bai yi nufinsa ba tare da rashin ikonsa akan tunkuɗe tilastawar, a wannan lokacin zunubi ko ƙunci ba zai faɗa kansa ba. Tare da lura da cewa matashiyar hadisin a abin da ke tsakanin bawa da Ubangijinsa ne, a kan aikata abinda aka haramta, amma barin abin da aka yi umarni akan mantuwa to ba zai saraya ba, amma da ace wani laifi zai faru akan aikinsa to ba zai sarayar da wani haƙƙi na abin halitta ba, kamar yadda da ace zai yi kisa akan kuskure, ko ya lalata wata mota akan kuskure to wajibi ne ya biya.

Fa’idoji
  1. Yalwar rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da tausasawarSa ga bayinSa inda ya ɗauke musu zunubi, idan saɓo ya bijiro daga garesu akan waɗan nan halayen uku.
  2. Falalar Allah ga Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma al'ummarsa.
  3. Ɗauke zunubi ba ya nufin ɗauke hukunci ko biya, misali wanda ya manta alwala, sai ya yi sallah yana mai zatan cewa shi yana da tsarki, to babu laifi a kansa da hakan, sai dai wajibi ne akansa ya yi alwala kuma ya sake sallar.
  4. Babu makawa a cikin ɗauke laifi da tilastawa daga samuwar sharuɗɗa, misali mai tilastawar ya zama mai iko akan zartar da abin da ya yi barazana da shi.
Madogara

الأربعون النووية (ص127) (ح39). سنن ابن ماجه (3/ 200) (2045). السنن الكبرى للبيهقي (7/ 584) (15094). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص89). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص382).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com