Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

LAFUZAN SAKI

Hadisai 1

Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ عَنْ أُمَّتِي مَا حَدَّثَتْ بِهِ أَنْفُسَهَا، مَا لَمْ تَعْمَلْ أَوْ تَتَكَلَّمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su abbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi ba'a kama shi da zancen zuci na sharri kafin ya aikata shi ko ya fade shi, yayin da Allah Ya ɗauke ƙunci kuma Ya yi afuwa, bai riƙi al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da abinda aka samu a cikin tinani da kaikawo a cikin zuciya ba, tare da ya nutsu gare shi kuma ya tabbata a wurinsa ba; idan ya tabbata a cikin zuciyarsa kamar girman kai ko taƙama ko munafunci ko ya yi aiki da gaɓɓansa ko ya faɗa da harshensa to cewa shi za'a kamashi da hakan.

Fa’idoji
  1. Allah - AlherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ƙetare kuma Ya yi afuwa daga tunani da zantukan zuci waɗanda suke ɗarsuwa a zuciya, sai mutum ya zantar da ransa da su, kuma su wuce haka akan tunani.
  2. Saki idam mutum ya yi tinaninsa, ya bijiro a cikin tinaninsa, sai dai bai fadama kowa ba kuma bai rubuta shi ba, to ba'a ɗaukarsa a matsayin saki.
  3. Zancen zuci ba'a kama mutum da shi duk girman da ya yi muddin dai bai tabbata a cikin ransa ba, ya yi aiki da shi ko ya zantar da shi.
  4. Girman darajar al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da keɓantarta da rashin kamawa da zancen zuci saɓanin al'ummun da suka gabata.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 46) (5269). صحيح مسلم (1/ 116) (127). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (7/ 560). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 46). توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (5/ 502). حاشية السندي على سنن ابن ماجه، للسندي (6/ 157). البدرُ التمام شرح بلوغ المرام، للمغربي (8/ 49).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com