Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

TASKACE SUNNAR ANNABI

Hadisai 3

Kada ku rubuta komai daga gare ni, kuma duk wanda ya rubuta wani abu daga gare ni ba Qur'ani ba to ya goge shi, kuma ku zantar daga gare ni kada ku samu damuwa, kuma duk wanda yayi mun qarya yana sane to ya tanadi mazauninsa a Wuta

عن أبي سعيد الخدري أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لا تكتبوا عني، ومَن كتب عني غيرَ القرآن فَلْيَمْحُه، وحدِّثوا عنِّي ولا حَرَج، ومَن كذب عليَّ -قال همام: أحسِبه قال: مُتعمِّدًا- فَلْيَتَبوَّأ مَقْعَدَه مِن النار».
Daga Abu Sa'id Al-Khudri Cewa Manzon Allah SAW ya ce: "Kada ku rubuta komai daga gare ni, kuma duk wanda ya rubuta wani abu daga gare ni ba Qur'ani ba to ya goge shi, kuma ku zantar daga gare ni kada ku samu damuwa, kuma duk wanda yayi mun qarya yana sane to ya tanadi mazauninsa a Wuta"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت. - مختار الصحاح، لزين الدين أبو عبد الله محمد بن أبي بكر بن عبد القادر الحنفي الرازي، تحقيق: يوسف الشيخ محمد، نشر: المكتبة العصرية - الدار النموذجية، بيروت – صيدا، لطبعة: الخامسة، 1420هـ - 1999م. - النهاية في غريب الحديث والأثر، لابن الأثير، نشر: المكتبة العلمية - بيروت، 1399هـ - 1979م، تحقيق: طاهر أحمد الزاوى - محمود محمد الطناحي. - إكمال المعلم بفوائد مسلم لعياض بن موسى بن عياض بن عمرون اليحصبي السبتي، المحقق: الدكتور يحيى إسماعيل، الناشر: دار الوفاء للطباعة والنشر والتوزيع، مصر، الطبعة: الأولى، 1419 هـ - 1998 م. - شرح سنن النسائي المسمى «ذخيرة العقبى في شرح المجتبى»، المؤلف: محمد بن علي بن آدم الإثيوبي الوَلَّوِي، الناشر: دار المعراج الدولية للنشر - دار آل بروم للنشر والتوزيع, الطبعة الأولى, 1416- 1424. - كشف المشكل من حديث الصحيحين، لجمال الدين أبي الفرج عبد الرحمن بن علي بن محمد الجوزي، المحقق: علي حسين البواب، الناشر: دار الوطن - الرياض.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su

عَنْ ‌أَبِي هُرَيْرَةَ عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ: «سَيَكُونُ فِي آخِرِ أُمَّتِي أُنَاسٌ يُحَدِّثُونَكُمْ مَا لَمْ تَسْمَعُوا أَنْتُمْ وَلَا آبَاؤُكُمْ، فَإِيَّاكُمْ وَإِيَّاهُمْ».
Daga Abu Huraira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - lallai ya ce: "Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wasu mutane a ƙarshen al'ummata za su bayyana suna ƙirƙirar ƙarya, kuma suna faɗin abin da wani kafinsu bai faɗa ba, suna ba da labarai da hadisan ƙarya abubuwan ƙirƙira, sai (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya umarcemu mu nisancesu kada mu zauna da su, kuma kada mu ji hadisansu; don kada ƙirƙirarran hadisin ya tabbata a cikin zukata, sai mu kasa kuɓuta daga su.

Fa’idoji
  1. A cikinsa akwai alama daga alamonin Annabta, yayin da Annabi - tsira da aminin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labain abin da zai afku a cikin al'ummarsa, sai ya afku kamar yadda ya ba da labari.
  2. Nisantar wanda zai yi ƙarya ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - haka kuma [da yin ta] ga Addinin Musulunci, da [buƙatar] kada a saurari ƙaryarsu.
  3. Gargaɗi game da karɓar Hadisai ko yaɗa su sai bayan tabbatarwa game da ingancinsu da tabbatarsu.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 12) (6)، قرة عين المحتاج في شرح مقدمة صحيح مسلم بن الحجاج (2/ 8).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya

عن عبدِ الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: كنتُ أكتبُ كلَّ شيءٍ أسمعُه من رسولِ الله صلَّى الله عليه وسلم أُريدُ حفْظَه، فنهتْني قريشٌ، وقالوا: أتكْتبُ كلَّ شيءٍ تَسمَعُه من رسول الله صلَّى الله عليه وسلم، ورسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم بَشَرٌ يتكلَّمُ في الغضَبِ والرِّضا؟ فأمسَكتُ عن الكتاب، فذكرتُ ذلك لرسول الله صلَّى الله عليه وسلم، فأومأ بإصبَعِه إلى فيه، فقال: «اكتُبْ، فوالذي نفسي بيدِه، ما يَخرُجُ منه إلا حقٌّ».
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkan abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son haddace shi, sai Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Shin ka dinga rubuta dukkan abin da ka ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, alhali Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin fushi da yarda? sai na dakata daga rubutun, sai na fadawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hakan sai ya yi nuni da 'yan yatsunsa zuwa bakinsa, sai ya ce: "Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abdullah ɗan Amr - Allah Ya yarada da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkanin abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - don na haddace shi a rubuce, sai wasu mutane daga Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin yarda da fushi, zai iya yin kuskure, sai na daina rubutun. Sai na ba wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - labarin abin da suka faɗa, sai ya yi nuni da danyatsansa zuwa bakinsa, sai ya ce; Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da yake fita daga cikinsa sai gaskiya a kowanne hali, haka a halin yarda da fushi. Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa game da AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Ba ya magana bisa son rai* shi (Alƙur'ani) ba wani abu ba ne ba ban da wahayi da ake saukar masa) [Al-najm 3-4].

Fa’idoji
  1. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ma'asumi (wanda ba ya laifi, kuma ba ya kuskure) ne a cikin abin da yake isar da shi daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - a halin yarda da fushi.
  2. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a kan kiyaye sunna da isar da ita.
  3. Halaccin rantsuwa ko da ba a sa a yi rantsuwar ba don maslaha, kamar ƙarfafa wani al'amari.
  4. Rubuta ilimi yana daga mafi muhimmancin dalilai da suke kiyaye ilimi.
Madogara

سنن أبي داود (5/ 489) (3646)، شرح سنن أبي داود للعباد (412/ 21).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com