Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga (tsawon) tafiyar shekara arba'in
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana narko mai tsanani a kan wanda ya kashe kafirin amana - shi ne kafiri wanda ya shiga garin musulunci bisa alƙawari da amincin - cewa ba zai shaƙi ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta yana kasancewa ne a kan nisan tafiyar shekara arba'in.
- Haramcin kashe kafirin amana da zimmi da musta'aman (wanda aka ba shi amincin ɗan wani lokaci) daga kafirai, kuma cewa hakan babban laifi ne daga manyan laifuka.
- Kafirin amana: Shi ne wanda aka yi alƙawari da shi daga kafirai a kan ya zauna a garinsa ba zai yaƙi musulamai ba su ma ba za su yaƙe shi ba. Zimmi kuma: Shi ne wanda ya zauna a garin musulmai ya ba da jizya. Musta'aman kuma: Shi ne wanda ya shiga garin musulmai a kan alkawari da aminci na wani ƙayyadajjen lokaci.
- Gargaɗi daga ha'intar alƙawurra (da aka ƙulla) tare da wanin musulmai.
صحيح البخاري منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 232). توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، للبسام (6/ 90). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 520). سبل السلام، لمحمد الصنعاني (2/ 501).