Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yaƙar kafirai, da yin ƙoƙari a fuskantarsu ta kowace hanya gwargwadan iko dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya, daga hakan: Na farko: Ciyar da dukiya a yaƙarsu; na siyan makamai da ciyarwa ga mayaƙa da makamancin hakan. Na biyu: Fita da rai da jiki dan haɗuwa da su da kuma tunkuɗesu. Na uku: Da kiransu ga wannan Addinin da harshe, da tsaida hujja akansu, da tsawatar da su da yi musu raddi.
- Kwaɗaitarwa akan yaƙar mushrikai da rai da dukiya da kuma harshe; kowa gwargwadan ikonsa, kuma yaƙi ba ya taƙaituwa akan yaki da rai kadai.
- Umarni da yaƙi na wajabci ne, zai iya zama wajibi aini (akan kowa da kowa), kuma zai iya zama wajibi kifa'i (wasu sun ɗaukewa wasu).
- Allah Ya shar’anta jihadi saboda wasu al'amura daga cikinsu: Na farko: Faɗa da shirka da mushrikai; domin cewa Allah ba Ya karɓar shirka har abada. Na biyu: Kawar da wahalhalun da suke bijirowa hanyar kira zuwa ga Allah. Na uku: Kiyaye aƙida daga dukkan abinda yake kishiyantarta. Na huɗu: Kariya ga musulmai da ƙasashensu da mutuncinsu da kuma dukiyoyinsu.
سنن أبي داود (4/ 158) (2504). سنن النسائي (6/ 7) (3096). مسند أحمد (19/ 272) (12246). صحيح مسلم (4/ 1935) (2490). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 442). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (6/ 336). منحة العلام شرح بلوغ المرام، عبد الله الفوزان (9/ 10). سبل السلام، لمحمد الصنعاني (2/ 460). مشكاة المصابيح، لمحمد التبريزي (2/ 1124).