Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ukkaz da Mijna da Thul-Majaz a lokacin Jahil;iyya Kasuwanni ne sai kuke ganin laifi ne kuyi kasuwanci a cikinsu lokacin aikin Hajji, Sai Allah ya saukar da: Babu laifi akan ku ku nemi Falala daga Ubangijinku" Bakara:198 a cikin lokacin Hajji

عن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما قال: كانت عُكَاظُ، ومَجِنَّةُ، وذُو المجَازِ أسوَاقَاً في الجاهلية، فَتَأَثَّمُوا أنْ يَتَّجِرُوا في المواسم، فنزلت: {ليس عليكم جناح أن تبتغوا فضلاً من ربكم} "البقرة" (198) في مواسم الحج.
An rawaito daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce: "Ukkaz da Mijna da Thul-Majaz a lokacin Jahil;iyya Kasuwanni ne sai kuke ganin laifi ne kuyi kasuwanci a cikinsu lokacin aikin Hajji, Sai Allah ya saukar da: Babu laifi akan ku ku nemi Falala daga Ubangijinku" Bakara:198 a cikin lokacin Hajji"
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wadan nan wurare sun kasancr kasuwanni ne ga Mushirikai kafin zuwan Musulunci suna yin kasuwanci a cikinta a lokutan Hajji, sai Sahabbai –Allah ya yarda das u- suka ji tsoron yin zunubi in sunyi kasuwanci a cikinta a lokacin aikin hajji, sai allah ya saukar da wannan Ayar don tayi musu bayanin Kasuwanci a cikin lokacin Aikin Hajji bat a bata aikin Hajji ta hanayar Shari’a, kan cewa Kasuwanci cikin Hajji halas ne, sai dai abun day a fi kuma yafi dacewa shi ne Mutum ya yi aikin Hajji ba tare da hada da komai ba, to wannan shi ne mafifici

Madogara

- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ. - صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض،1426هـ. - كنوز رياض الصالحين، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا، الطبعة الأولى 1430ه. - تطريز رياض الصالحين؛ تأليف فيصل آل مبارك، تحقيق د. عبد العزيز آل حمد، دار العاصمة-الرياض، الطبعة الأولى، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HUKUNCE-HUKUNCE DA MAS'ALOLIN HAJJI DA UMRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com