Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Rulings of the Prophet's Mosque

Hadisai 1

Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma

عَنْ ‌أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «صَلَاةٌ فِي مَسْجِدِي هَذَا خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ صَلَاةٍ فِيمَا سِوَاهُ إِلَّا الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar sallah a masallacinsa, kuma cewa shi yafi yawan lada daga sallah dubu a cikin waninsa daga masallatan duniya, sai dai Masallaci mai alfarma a Makka, shi ne mafifici daga sallah a cikin masallacinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Fa’idoji
  1. Ruɓanya ladan sallah a cikin Masallaci mai alfarma, da masallacin Annabi.
  2. Sallah a Masallaci mai alfarma ita ce mafi alheri daga sallah dubu a wasu masallatan da ba su ba.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 60) (1190)، صحيح مسلم (2/ 1012) (1394)، فتح الباري (3/67)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (24/ 684).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com