Allah ka jikan masu yin aski, sai suka ce: da masu saisaye ya manzon Allah? sai ya ce: Allah ka jikan masu aski, sai suka ce: da masu saisaye ya manzon Allah? sai ya kuma cewa: Allah ka jikan masu aski, sai suka ce: da masu saisaye ya manzon Allah? sai ya ce da masu saisaye.
Aski ko saisaye na daga cikin ibadun aikin Hajji da Umara, amma yin aski yafi saisaye falala saboda shi ne mai kaiwa matuka a cikin bauta, da nuna kaskanchi ga Allah madaukakin sarki, ta hanyar katse gashin kai yana cikin biyayya ga Allah madaukakin sarki, saboda hakanan lallai Annabi mai tsira da aminchin Allah su kara tabbata a gareshi yayi addu`ar naman jin kai ga masu aski har sau uku, wadanda suke tare da shi suna ambato masa masu saisaye sai ya rabu da su, sai a ta uku ko ta hudu ya shigar da masu saisaye tare da su cikin addu`ar, wannan na yin nuni bisa cewa lallai yin aski a cikin hakkin maza shi yafi falala amma wannan yin askin idan bai kasance a umara ta tamattu`i ba saboda lokacin yayi kadan ta yanda za`ace wani gashin ya fito kafin ayi askin Hajji, yin saisaye a cikin hakkin sa shi yafi; domin cewa shi zai yi aski bayan haka
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ، 2006م. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ، 2005م. الإفهام في شرح عمدة الأحكام لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة: الأولى 1435هـ. خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، فيصل بن عبد العزيز المبارك، الطبعة: الثانية 1412هـ، 1992م. صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، القاهرة، الطبعة: الأولى 1427هـ.