Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HUKUNCE-HUKUNCEN IHRAMI

Hadisai 2

Mun iso tare da -Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma mu cewa: Amsawarka da Hajji to sai Annabi- Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya Umarce mu sai Muka Maida ita.

عن جابرٍ رضي الله عنه قال: قدِمنا مع رسولِ الله صلى الله عليه وسلم ، ونحنُ نقولُ: لبيك بالحجِّ، فأمرَنا رسولُ الله صلى الله عليه وسلم فجعلناها عُمرةً.
Daga Jabir -Allah ya yarda da shi- ya ce Mun iso tare da Manzon Allah -Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma mu muna cewa Amsarka Hajji, Sai Manzon Allah -Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya Umarce mu sanya ta Umra.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Jabir yana bamu bamu labari -Allah ya yarda da shi cewa sun iso tare da Manzon Allah -Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- a Hajjin bankwana mafi yawansu kuma suna cewa: "Amsawarka aikin Hajji" ai suna cewa sunyi Ifradin Hajji to sai Annabi -Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya Umarci wanda duk bai tanadi Hadaya daga cikin su, kan ya warware Hajjinsa zuwa Umra; don su koma masu Hajjin Tamattu'i, sai suka yi hakan- Allah ya yarda da su.

Madogara

عمدة الأحكام، تأليف: عبد الغني بن عبد الواحد المقدسي، تحقيق: محمود الأرناؤوط، دار الثقافة العربية ومؤسسة قرطبة، الطبعة الثانية، 1408هـ. تيسير العلام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق محمد صبحي بن حسن حلاق، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة العاشرة، 1426 هـ. تأسيس الأحكام شرح عمدة الأحكام، تأليف: أحمد بن يحي النجمي: نسخة إلكترونية لا يوجد بها بيانات نشر. تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة الأولى: 1426هـ. الإفهام في شرح عمدة الأحكام، للشيخ عبد العزيز بن عبد الله بن باز، تحقيق: سعيد بن علي بن وهف القحطاني، الطبعة الأولى، 1435 هـ خلاصة الكلام على عمدة الأحكام، تأليف: فيصل بن عبد العزيز آل مبارك، الطبعة الثانية، 1412 هـ الإلمام بشرح عمدة الأحكام، تأليف: إسماعيل الأنصاري، مطابع دار الفكر، الطبعة الأولى: 1381 هـ صحيح البخاري ، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ صحيح مسلم ، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa Talbiyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "AmsawarKa ya Allah, amsawarKa, amsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa, lallai cewa godiya da ni'ima na Ka ne kuma mulki ma naKa ne, baKa da abokin tarayya

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا: أَنَّ تَلْبِيَةَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَبَّيْكَ اللهُمَّ، لَبَّيْكَ، لَبَّيْكَ لَا شَرِيكَ لَكَ لَبَّيْكَ، إِنَّ الْحَمْدَ وَالنِّعْمَةَ لَكَ وَالْمُلْكَ لَا شَرِيكَ لَكَ» قَالَ: وَكَانَ عَبْدُ اللهِ بْنُ عُمَرَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا يَزِيدُ فِيهَا: لَبَّيْكَ لَبَّيْكَ، وَسَعْدَيْكَ، وَالْخَيْرُ بِيَدَيْكَ، لَبَّيْكَ وَالرَّغْبَاءُ إِلَيْكَ وَالْعَمَلُ.
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Talbiyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "AmsawarKa ya Allah, amsawarKa, amsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa, lallai cewa godiya da ni'ima na Ka ne kuma mulki ma naKa ne, baKa da abokin tarayya" Ya ce: Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance yana ƙarawa a cikinta: AmsawarKa amsawarKa, da taimakonKa (akan aiki), alheri yana hannayenKa, amsawarKa fata yana gareKa da kuma aiki.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Talbiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance idan ya yi nufin shiga aikin Hajji ko Umarah ita ce ya ce: (AmsawarKa ya Allah amsawarKa) amsawa ta lazimi gareKa bayan amsawa a cikin abinda Ka kiramu na ikhlasi da tauhidi da hajji da wasunsu, (AmsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa) Kaine Kai kaɗai wanda ka cancanci a bauta maka, baKa da abokin tarayya a rububiyyarKa da UluhiyyarKa da sunayenKa da siffofinKa, (lallai cewa godiya) da godiya da yabo (da ni'ima) daga gareKa Kaine Mai bada su (gareKa ne) ana juya su a kowane hali, (mulki ma) kamar haka naKa ne, (baKa da abokin tarayya) dukkansu naKa ne Kai kaɗai. Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance yana ƙarawa a cikinta: (AmsawarKa amsawarKa da taimakonKa) Ka taimakeni taimako bayan taimako, (alheri yana hannayenKa) dukkansa kuma daga falalarKa ne, (amsawarKa fata gareKa ne) da nema da tambaya zuwa wanda alheri yake a hannunSa, (aiki ma) gareKa ne Kaine wanda ya cancanci a bauta masa.

Fa’idoji
  1. Shar’antuwar Talbiyyah a Hajji da Umarah, da ƙarfafuwarta a cikinsa; domin ita Talbiya alamarsa ce keɓantacciya, kamar kabbara alama ce ta sallah.
  2. Ibnul Munir ya ce: A cikin Shar’antuwar Talbiyyah akwai faɗakarwa akan girmamawa ga Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa cewa taruwarsu a ɗakinSa kaɗai ya kasance ne da kira daga gareShi - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
  3. Abinda ya fi shi ne lazimtar Talbiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma babu laifi da ƙari dan tabbatarwar Annabi - tsira da aminci su tabbata gare shi - ga karin. Ibnu Hajar ya ce: Wannan shi ne mafi daidaituwar fuskoki, sai a ware abinda ya zo Marfu'i, idan ya zaɓi faɗar abinda ya zo Mauƙufi ko shi ya farar da shi da kansa daga abinda ya dace to ya faɗe shi a ware dan kada ya cakuɗa da Marfu'i, sai ya yi kama da halin addu'a a tahiya, cewa shi ya ce a cikinsa; Sannan ya zaɓi abinda ya so na roƙo da yabo: wato bayan ya gama da Marfu'in.
  4. An so ɗaga murya a Talbiyya, wannan a haƙƙin namiji ne kadai, amma mace sai ta ƙanƙar da muryarta dan tsoron fitina.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 138) (1549). صحيح مسلم (2/ 841) (1184). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص370). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (3/ 498).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com