Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya lazimci i'itikafi a goman ƙarshe na Ramadan, dan neman Lailatul Qadr, kuma ya zarce akan hakan har zuwa lokacin da Allah Ya ɗauki ransa, haƙiƙa matansa - Allah Ya yarda da su - sun lazimci i'itikafi a bayansa.
- Halaccin i'itikafi a cikin masallatai, har ga mata akan wasu iyakoki na shari'a, da kuma sharaɗin aminta daga fitina.
- I'itikafi yana ƙarfafa a cikin goman ƙarshe na Ramadan saboda lazimtar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- I'itikafi Sunna ne mai zarcewa ba'a shafe shi ba, dan matansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun yi i'itikafi a bayansa.
صحيح البخاري (3/ 47) (2026). صحيح مسلم (2/ 831) (1172). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص351). تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 474).