Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta

عَنْ أَبِي عُبَيْدٍ، مَوْلَى ابْنِ أَزْهَرَ، قَالَ: شَهِدْتُ العِيدَ مَعَ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، فَقَالَ: هَذَانِ يَوْمَانِ نَهَى رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ صِيَامِهِمَا: يَوْمُ فِطْرِكُمْ مِنْ صِيَامِكُمْ، وَاليَوْمُ الآخَرُ تَأْكُلُونَ فِيهِ مِنْ نُسُكِكُمْ.
Daga Abu Ubaid, 'yantaccen Ibnu Azhar, ya ce: Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani game da azimin ranar idin ƙaramar sallah da idin babbar sallah; amma idin ƙaramar sallah to ranar buɗa baki ce daga azimin watan Ramadan, amma ranar idin babbar sallah to ranar ci ce daga abubuwan layya.

Fa’idoji
  1. Haramcin azimin ranakun idin ƙaramar sallah da babba da kwanukan Tashriƙ; domin cewa su masu bi ne ga ranar babbar sallah sai dai ga wanda bai samu hadaya ba to azimin kwanukan tashriƙ ya halatta gare shi.
  2. Ibnu Hajar ya ce: An ce: Fa'idar siffanta ranaku biyun dan nuni ga illa a wajabcin cin abinci a cikinsu, shi ne rabewa daga azimi, da bayyanar cikarsa shi kaɗai da karya azimin abinda ke bayansa, ɗayan kuma saboda yanka wanda ake neman kusanci da yankansa dan a ci daga gare shi.
  3. An so ga mai huɗuba (liman) a cikin huɗubarsa ya tinatar da abinda yake rataye da lokacinsa na hukunce-hukunce kuma ya kintaci munasabobi.
  4. Halaccin ci daga abin yanka.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 42) (1990). صحيح مسلم (2/ 799) (1137). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص344). تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 461). الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص426). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص161).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ABIN DA YAKE HARAMTA A KAN MAI AZUMI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com