Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Azimi a halin tafiya bai zama daga aikin alheri ba

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَرَأَى زِحَامًا وَرَجُلًا قَدْ ظُلِّلَ عَلَيْهِ، فَقَالَ: «مَا هَذَا؟»، فَقَالُوا: صَائِمٌ، فَقَالَ: «لَيْسَ مِنَ البِرِّ الصَّوْمُ فِي السَّفَرِ»، وَفِي لَفْظٍ لِمُسلِمٍ: «عَلَيْكُمْ بِرُخْصَةِ اللهِ الَّذِي رَخَّصَ لَكُمْ».
Daga Jabir ɗan Abdullah -Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a wata tafiya, sai ya ga cunkoso da wani mutum an yi masa inuwa, sai ya ce: «Menene wannan», sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: «Azimi a halin tafiya bai zama daga aikin alheri ba». A cikin wani lafazin na Muslim: «Na horeku da rangwamin da Allah Ya yi muku».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wata tafiya, sai ya ga wani mutum mutane sun haɗu a kansa alhali an yi masa inuwa saboda zafin rana da tsananin ƙishirwa, sai ya ce: Me ya same shi ? sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: Azimi a halin tafiya bai zama daga cikin ayyukan alheri ba, na horeku da rangwamin da Allah Yayi muku.

Fa’idoji
  1. Bayanin sauƙin shari'ar Musulunci.
  2. Halaccin yin Azumi a halin tafiya, da kuma halaccin riƙo da rangwami da barin yin azimin.
  3. An hana yin azumi a halin tafiya idan azumin yana yi masa wahala, muddin dai bai kai iyakar mutuwa ba sai (azimin) ya haramta.
  4. Nawawi ya ce: Ba aikin alheri ba ne ku yi azimi a halin tafiya: ma'anarsa: Idan azumin yana yi muku wahala, kuma kuka ji tsoron cuta, siyaƙin hadisin yana hukunta wannan tawilin.
  5. Kulawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa da yadda yake tambayar halayensu.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 34) (1946). صحيح مسلم (2/ 786) (1115). تيسير العلام، للبسام (ص327). تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 433).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
AZUMIN MASU UZURI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com