Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana alamar shigar watan Ramadan da kuma fitarsa, sai ya ce: Idan kun ga injirin watan Ramadan to ku azimce shi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwanaki talatin na watan Sha'aban, idan kun ga jinjirin watan Shawwal to ku ajiye azumi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwana talatin ga watan Ramadan.
- Dogara a tabbatar da shigar wata akan gani ne ba akan lissafi ba.
- Ibunl Munzir ya cirato ijma'i akan cewa azimi ba ya wajaba idan shigar watan Ramadan ya kasance da lissafi ne kawai ba ganin (wata) ba.
- Wajabcin cika Sha'aban kwana talatin idan girgije ko makancinsa ya tsare ganin jinjirin watan Ramadan.
- Watan sama ba ya kasancewa sai kwana ashirin da tara, ko kwanaki talatin.
- Wajabcin cika Ramadan kwanaki talatin idan girgije ko waninsa ya tsare (ganin) jinjirin watan Shawwal.
- Wanda yake a wurin da babu wanda yake bibiyar al'amarin musulmai a sha'anin azimi, ko akwai wanda bai kula da hakan ba to yana kamata ya kiyaye hakan ya bibiye shi da wanda hakan yake tabbata a wurinsa da ganin kansa ko da ganin wanda ya aminta da shi; sai ya yi azimi da hakan kuma yasha ruwa.
صحيح البخاري (3/ 25) (1900). صحيح مسلم (2/ 760) (1080). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص314). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (3/ 414). الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص385). خلاصة الكلام على عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص146). الموسوعة الفقهية الكويتية (23/ 142).