Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan kun so zan baku ita, babu rabo a cikinta ga mawadaci, ko ƙaƙƙarfan da yake iya neman na kansa

عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ عَدِيِّ بْنِ الخِيَارِ قَالَ: أَخْبَرَنِي رَجُلَانِ أَنَّهُمَا أَتَيَا النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي حَجَّةِ الوَدَاعِ وَهُوَ يُقَسِّمُ الصَّدَقَةَ، فَسَأَلَاهُ مِنْهَا، فَرَفَّعَ فِينَا البَصَرَ وَخَفَّضَهُ، فَرَآنَا جَلْدَيْنِ، فَقَالَ: «إِنَّ شِئْتُمَا أَعْطَيْتُكُمَا، وَلَا حَظَّ فِيهَا لِغَنِيٍّ، وَلَا لِقَوِيٍّ مُكْتَسِبٍ».
Daga Ubaidullahi Ibnu Adi Ibnul Khiyar ya ce: Wasu mutane biyu sun bani labarin cewa sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Hajjin ban kwana alhali shi yana raba sadaka (zakka), sai suka tambaye shi zakkar, sai ya ɗaga idanuwansa garemu ya kuma yi ƙasa da su, sai ya ganmu ƙarfafa ne, sai ya ce: «Idan kun so zan baku ita, babu rabo a cikinta ga mawadaci, ko ƙaƙƙarfan da yake iya neman na kansa».
Abu Dawud da Nasa'i ne suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wasu mutane biyu sun zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Hajjin ban kwana, alhali shi yana raba sadaka (zakka), kuma suka nemi ya basu daga cikin zakkar, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sake kallonsu, dan ya gane halinsu, kuma shin ya halatta a basu sadakar ko a'a? Sai ya gansu mazaje ne biyu ƙarfafa, sai ya ce: Idan kuna so zan baku daga cikin zakkar, babu rabo a cikinta ga wanda yake da dukiyar da zata ishe shi, ko ga wanda yake da ikon yin aiki ko juya dukiya, ko da ba shi da dukiyar da za'a ɗauke shi (a matsayin) mawadaci da ita.

Fa’idoji
  1. Haramcin roƙo ga mutum mawadaci ko ƙaƙƙarfan da zai iya neman na-kansa.
  2. Asali ga wanda ba’a san yana da dukiyaba to talaka ne da kuma cancantar karɓar sadaka.
  3. Mujarradin ƙarfi ba ya hukunta rashin cancantar karɓar sadaka, kai babu makawa da a haɗa da iko akan iya nema.
  4. Mai iko akan neman abin da zai ishe shi ba ya halatta ya karɓi sadaka ta wajibi (wato Zakkah); dan wadatuwarsa da neman na kansa, kamar wadatuwar mawadaci ne da dukiya.
  5. Tarbiyyar Annabi mai girma ga mutum musulmi akan kamewa, da kuma bayarwa banda karɓa da roƙo da kuma kasala.
Madogara

سنن أبي داود (3/ 75) (1633). سنن النسائي (5/ 99) (2598). ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (23/ 210). شرح أبي داود للعيني (6/ 374).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
WURAREN MIƘA ZAKKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com