عن أبي سعيد الْخُدْرِي رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «ليس فيما دون خمس أَوَاقٍ صدقة، ولا فيما دون خمس ذَوْدٍ صدقة، ولا فيما دُونَ خمسة أَوْسُقٍ صدقة».
Daga Abu Sa'id Al'khudri -Allah ya yarda da shi- ya ce Manzon Allah - Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce : "abu Zakka a kasa da Ukiyya Biyar , ko kuma kasa da Rakuma Biyar, ko kasa da Buhu biyar."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Zakka: Yalwatawa ce tsakanin Mawadata da Mabukata, Kuma don haka ne ma ba'a karba daga wanda kudinsa basu taka kara sun karya ba don ba'a daukarsa Mawadaci.To kuma Sharia ta bayyana Mafi karancin abinda ya Wajaba ayi Zakka a kansa, amma kuma Duk wanda ya Mallaki kasa da Mafi karancin Haddin Zakka, to cewa shi Mabukaci ba'a karbar komai daga Wurinsa, to Ma'abocin Azurfa, Bai wajaba akansa Zakka har Sai ya kasance yana da Ukiyya biyar, kuma Ukiyya ita ce Dirhami Arba'in, to sai ya kasance Nisabin Zakkarsa a ciki Dirhami Dari biyu, wanda yayi daidai da Gram Dari biyar da Casa'in, kuma Mai zakkar Rakumabata wajaba akansa ba, har sai yana da Rakuma Biyar ko sama da haka, kuma kasa da haka babu zakka a ciki. kuma Mai Zakkar kayan Gonababu zakka a kansa sai ta kai Buhu biyar, kuma Buhu shi ne kwano Sittin, to sai ya kasance Nisabinsa shi Kwano Dari Uku.
Madogara
عمدة الأحكام، تأليف: عبد الغني بن عبد الواحد المقدسي، تحقيق: محمود الأرناؤوط، دار الثقافة العربية ومؤسسة قرطبة، الطبعة الثانية، 1408هـ.
تيسير العلام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق محمد صبحي بن حسن حلاق، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة العاشرة، 1426هـ.
تأسيس الأحكام شرح عمدة الأحكام، تأليف: أحمد بن يحي النجمي: نسخة إلكترونية لا يوجد بها بيانات نشر.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة الأولى: 1426هـ.
الإفهام في شرح عمدة الأحكام، للشيخ عبد العزيز بن عبد الله بن باز، تحقيق: سعيد بن علي بن وهف القحطاني، الطبعة الأولى، 1435هـ.
خلاصة الكلام على عمدة الأحكام، تأليف: فيصل بن عبد العزيز آل مبارك، الطبعة الثانية، 1412هـ.
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، تأليف: إسماعيل الأنصاري، مطابع دار الفكر، الطبعة الأولى: 1381هـ.
صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ.
صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ مُعَاذٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَمَّا وَجَّهَهُ إِلَى الْيَمَنِ أَمَرَهُ أَنْ يَأْخُذَ مِنَ الْبَقَرِ مِنْ كُلِّ ثَلَاثِينَ تَبِيعًا أَوْ تَبِيعَةً، وَمِنْ كُلِّ أَرْبَعِينَ مُسِنَّةً، وَمِنْ كُلِّ حَالِمٍ -يَعْنِي مُحْتَلِمًا- دِينَارًا أَوْ عَدْلَهُ مِنَ المَعَافِرِ، ثِيَابٌ تَكُونُ بِالْيَمَنِ.
Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi -: Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika shi zuwa Yaman sai ya umarce shi ya karɓi Tabi'i namiji ko mace (wanda yake bin uwarsa kiwo) daga dukkan (shanu) talatin, haka (ya karɓi) Musinnah daga dukkanin (shanu) arba'in, daga (ya karɓi) dinari ɗaya ko kwatankwacinsa na Ma'afir wasu tufa ne na Yaman daga duk wanda ya isa mafarki.
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika Mu'az ibnu Jabal - Allah Ya yarda da shi - zuwa Yaman dan koyar da mutane da kuma kiransu, daga cikin abin da ya umarce shi da shi shine ya karɓi Zakkar shanunsu tabi'i ɗaya namiji ko mace daga dukkanin talatin; shine wanda ya cika shekara ɗaya, haka (ya karɓi) Musinna daga dukkanin arba'in; ita ce wacce ta cika shekara biyu. Kuma ya karɓi jizyar dinari ɗaya daga mazowa littafi Yahudawa da Nasara daga dukkanin namiji baligi, ko abin da ya yi daidai da dinari ɗaya na tufafin Yaman waɗanda ake kiransu da: Ma'afirri.
Fa’idoji
- Ba'a karɓar jizya sai daga wanda ya isa mafarki; domin cewa ƙa'idar wanda ba'a karɓa daga gare shi ita ce: Shine wanda ba ya halatta a kashe shi idan an ribace shi: Daga ƙaramin yaro, da mace, da wasunsu.
- Ƙimanta jizyar yana komawa ne ga ijtihadin liman, domin ita tana saɓawa gwargwadan saɓawar guri da kuma zamani, da wadata da kuma talauci, dalili akan haka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne wanda ya ƙaddara gwargwadanta ga mutanen Yaman, sai ya ce wa Mu'az; "Ka karɓi dinari ɗaya daga dukkanin wanda ya isa mafarki" yayin da jizya ta ƙaru lokacin Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ƙayyade gwargwadanta ga mutanen Sham.
- Himmatuwa da tara Zakkah, da kuma wakilta wanda zai tattarota yana daga cikin muhimman ayyukan shugaba.
- Tabi'i: Shi ne wanda ya cika shekara ɗaya, ya shiga cikin shekara ta biyu, kuma an ambace shi tabi'i ne; domin shi bai gushe ba yana bin uwarsa kiwo.
- Dinari: Kuɗi ne na zinari, dinari na Musulunci: Awonsa shine Gram huɗu da rubu'in zinari (4.25GM).
Madogara
سنن أبي داود (3/ 26) (1576).
سنن الترمذي (2/ 13) (623).
سنن النسائي (5/ 25) (2450 - 2451).
سنن ابن ماجه (3/ 22) (1803).
فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (3/ 35).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (3/ 297).
سبل السلام، للصنعاني (1/ 517 ).
Wannan hadisi a HadeethEnc.com