Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

WAJIBCIN ZAKKKA DA HUKUNCIN MAI ƘIN BAYARWA

Hadisai 4

Babu wani ma'abocin zinare ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai a ranar alƙiyama ya kasance za'a ƙerasu a siffar alluna na wuta

عَنْ أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا مِنْ صَاحِبِ ذَهَبٍ وَلَا فِضَّةٍ، لَا يُؤَدِّي مِنْهَا حَقَّهَا، إِلَّا إِذَا كَانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ، صُفِّحَتْ لَهُ صَفَائِحُ مِنْ نَارٍ، فَأُحْمِيَ عَلَيْهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ، فَيُكْوَى بِهَا جَنْبُهُ وَجَبِينُهُ وَظَهْرُهُ، كُلَّمَا بَرَدَتْ أُعِيدَتْ لَهُ، فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ، حَتَّى يُقْضَى بَيْنَ الْعِبَادِ، فَيَرَى سَبِيلَهُ، إِمَّا إِلَى الْجَنَّةِ، وَإِمَّا إِلَى النَّارِ» قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، فَالْإِبِلُ؟ قَالَ: «وَلَا صَاحِبُ إِبِلٍ لَا يُؤَدِّي مِنْهَا حَقَّهَا، وَمِنْ حَقِّهَا حَلَبُهَا يَوْمَ وِرْدِهَا، إِلَّا إِذَا كَانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ، بُطِحَ لَهَا بِقَاعٍ قَرْقَرٍ، أَوْفَرَ مَا كَانَتْ، لَا يَفْقِدُ مِنْهَا فَصِيلًا وَاحِدًا، تَطَؤُهُ بِأَخْفَافِهَا وَتَعَضُّهُ بِأَفْوَاهِهَا، كُلَّمَا مَرَّ عَلَيْهِ أُولَاهَا رُدَّ عَلَيْهِ أُخْرَاهَا، فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ، حَتَّى يُقْضَى بَيْنَ الْعِبَادِ، فَيَرَى سَبِيلَهُ إِمَّا إِلَى الْجَنَّةِ، وَإِمَّا إِلَى النَّارِ» قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، فَالْبَقَرُ وَالْغَنَمُ؟ قَالَ: «وَلَا صَاحِبُ بَقَرٍ، وَلَا غَنَمٍ، لَا يُؤَدِّي مِنْهَا حَقَّهَا، إِلَّا إِذَا كَانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ بُطِحَ لَهَا بِقَاعٍ قَرْقَرٍ، لَا يَفْقِدُ مِنْهَا شَيْئًا، لَيْسَ فِيهَا عَقْصَاءُ، وَلَا جَلْحَاءُ، وَلَا عَضْبَاءُ تَنْطَحُهُ بِقُرُونِهَا وَتَطَؤُهُ بِأَظْلَافِهَا، كُلَّمَا مَرَّ عَلَيْهِ أُولَاهَا رُدَّ عَلَيْهِ أُخْرَاهَا، فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ، حَتَّى يُقْضَى بَيْنَ الْعِبَادِ، فَيَرَى سَبِيلَهُ إِمَّا إِلَى الْجَنَّةِ، وَإِمَّا إِلَى النَّارِ» قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، فَالْخَيْلُ؟ قَالَ: «الْخَيْلُ ثَلَاثَةٌ: هِيَ لِرَجُلٍ وِزْرٌ، وَهِيَ لِرَجُلٍ سِتْرٌ، وَهِيَ لِرَجُلٍ أَجْرٌ، فَأَمَّا الَّتِي هِيَ لَهُ وِزْرٌ، فَرَجُلٌ رَبَطَهَا رِيَاءً وَفَخْرًا وَنِوَاءً عَلَى أَهْلِ الْإِسْلَامِ، فَهِيَ لَهُ وِزْرٌ، وَأَمَّا الَّتِي هِيَ لَهُ سِتْرٌ، فَرَجُلٌ رَبَطَهَا فِي سَبِيلِ اللهِ، ثُمَّ لَمْ يَنْسَ حَقَّ اللهِ فِي ظُهُورِهَا وَلَا رِقَابِهَا، فَهِيَ لَهُ سِتْرٌ وَأَمَّا الَّتِي هِيَ لَهُ أَجْرٌ، فَرَجُلٌ رَبَطَهَا فِي سَبِيلِ اللهِ لِأَهْلِ الْإِسْلَامِ، فِي مَرْجٍ وَرَوْضَةٍ، فَمَا أَكَلَتْ مِنْ ذَلِكَ الْمَرْجِ، أَوِ الرَّوْضَةِ مِنْ شَيْءٍ، إِلَّا كُتِبَ لَهُ، عَدَدَ مَا أَكَلَتْ حَسَنَاتٌ، وَكُتِبَ لَهُ، عَدَدَ أَرْوَاثِهَا وَأَبْوَالِهَا، حَسَنَاتٌ، وَلَا تَقْطَعُ طِوَلَهَا فَاسْتَنَّتْ شَرَفًا، أَوْ شَرَفَيْنِ، إِلَّا كَتَبَ اللهُ لَهُ عَدَدَ آثَارِهَا وَأَرْوَاثِهَا حَسَنَاتٍ، وَلَا مَرَّ بِهَا صَاحِبُهَا عَلَى نَهْرٍ، فَشَرِبَتْ مِنْهُ وَلَا يُرِيدُ أَنْ يَسْقِيَهَا، إِلَّا كَتَبَ اللهُ لَهُ، عَدَدَ مَا شَرِبَتْ، حَسَنَاتٍ» قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، فَالْحُمُرُ؟ قَالَ: «مَا أُنْزِلَ عَلَيَّ فِي الْحُمُرِ شَيْءٌ، إِلَّا هَذِهِ الْآيَةَ الْفَاذَّةُ الْجَامِعَةُ»: {فَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ، وَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ} [الزلزلة: 8].
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani ma'abocin zinare ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai a ranar alƙiyama ya kasance za'a ƙerasu a siffar alluna na wuta, sai a ƙona shi a kansu a cikin wutar Jahannama, sai a yi wa sasanninsa da goshinsa da bayansa lalas, duk lokacin da suka ƙone sai a dawo da su, a cikin wani yinin da gawargwadansa shekara dubu hamsin ne, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, sai yaga hanyarsa, ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta". Aka ce : Ya Manzon Allah, to raƙuma fa? ya ce: "Ko ma'abocin raƙuma da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, yana daga haƙƙinsu tatsar nonnuwansu lokacin gangarowarsu (ruwa), sai ya kasance a ranar lahira za'a shinfiɗa su a ƙasa miƙaƙƙiya, mafi cikar abinda da suke, ba zai rasa wani ɗan maraƙi ɗaya ba, zasu dinga taka shi da kofatansu, kuma zasu dinga cizansa da bakunansu, duk lokacin da na farkonsu ya shuɗe a kansa sai a dawo da na ƙarshensu, a cikin wani yinin da ya kasance gwargwadansa shekara dubu hamsin ne, har sai an yi hukunci tsakanin mutane, sai ya ga hanyarsa ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta". Aka ce: Ya Manzon Allah, to shanu da tumakai fa? ya ce: "Ko ma'abocin shanu, ko tumakai, ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai ranar lahira ya kasance an shinfiɗa musu mikaƙƙiyar ƙasa, ba zai rasa wani abu daga cikinsu ba, babu wata mai lanƙwasasshen ƙaho, ko mara ƙaho, ko mai karyayyen ƙaho zasu dinga sukarsa da ƙahonhunansu, kuma zasu dinga taka shi da kofatansu, duk lokacin da na farkonsu ya wuce a kansa za'a dawo da na ƙarshensu, a cikin wata ranar da gwargwadanta ya kai shekara dubu hamsin, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, zai ga hanyarsa ko dai zuwa aljanna, ko kuma zuwa wuta" Aka ce : Ya Manzon Allah, to doki fa? ya ce: "Doki uku ne: (Doki) laifi ne ga wani mutumin, kuma su sutura ne ga wani mutumin, kuma su lada ne ga wani mutumin. Amma waɗanda suke su laifi ne gare shi, shi ne mutumin da ya ɗauresu dan riya da alfahari da ƙiyayya ga ma'abota Musulunci, to su laifi ne akansa, amma waɗanda su sutura ne gare shi, to shi ne mutumin da ya ɗauresu saboda Allah, sannan bai manta haƙƙin Allah a bayayyakinsu ko wuyayensu ba, to su sutura ne gare shi, amma waɗanda su lada ne gare shi, shi ne mutumin da ya ɗauresu saboda Allah dan ma'abota Musulunci, a cikin ciyayi da dausayi, duk abinda suka ci na wancan ciyayin ko dausayin, sai an rubuta masa kyakkyawan lada adadin abinda suka ci, kuma an rubuta masa kyakkyawan lada adadin torosonsu da fitsarinsu, ba zaka yanke igiyarsu ba su yi sukuwa tsawon saki daya ko biyu, sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa n lada adadin gurbinsu da torosonsu, kuma ma'abocinsu bai wuce akan wata korama ba, su sha daga gareta kuma ba ya nufin ya shayar da su, sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa adadin abinda suka sha"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana nau'ika na dukiya, da sakamakon wanda bai bada zakkarsu ba a ranar alƙiyama, daga cikinsu: Na farko: Zinare da azirfa da abinda ke cikin hukuncinsu na dukiyoyi da hajoji na kasuwanci, shi ne abinda zakka ta wajaba a cikinsa bai bayar ba, idan ranar alƙiyama ta zo za'a narka su aƙerasu akan siffar alluna, kuma a kunna wutar Jahannama a kansu, a yi masa azaba da su, sai a yi wa sasanninsa da goshinsa da bayansa lalas da su, duk lokacin da suka yi sanyi sai a dawo da ƙunarsu, zai kasance a wannan halin na azaba tsawon ranar alkiyama wanda gwargwadan yininta shekara dubu hamsin ne, har sai Allah Ya yi hukunci tsakanin halitta, sai ya zama daga 'yan aljanna ko daga 'yan wuta. Na biyu: Wanda ya mallaki raƙuman da ba ya bada farillar zakkarsu da kuma haƙƙinsu, daga ciki (akwai) tatsar nonansu ga wanda ya zo nema cikin miskinai, za’a zo da waɗannan raƙuman masu girma masu ƙiba kuma mafi yawa kan yadda suke a cikin adadinsu, za'a shinfiɗa shi a jefa shi a miƙar da mai su ranar alƙiyama akan wata ƙasa mai yalwa miƙaƙƙiya, zasu dinga takashi da ƙafafunsu, kuma zasu dinga cizonsa da haƙoransu, duk lokacin da na ƙarshensu ya wuce akansa za'a dawo da na farkonsu a kansa, zai zarce akan wannan halin na azaba tsawon yinin alƙiyama wace gwargwadan yininta shekara dubu hamsin ne, har sai Allah Ya yi hukunci tsakanin halitta, sai ya zama daga 'yan aljanna ko daga 'yan wuta. Na uku: Wanda ya mallaki shanu da tumakai - wadanda suke tunkiyoyi da awakai - waɗanda mai su ba ya bada zakkarsu ta wajibi, za’a zo da su mafi yawan abinda da suke akai na adadi ba za’a tauye komai ba daga garesu, sai a shinfiɗasu a jefa shi kuma a miƙar da mai su a ranar lahira akan ƙasa mai yalwa madaidaiciya, babu wasu masu lanƙwasasshen ƙaho, ko waɗanda ba su da ƙahon, ko masu karyayyen ƙaho, kai su akan mafi cikar siffofinsu ne, sai su soke shi da ƙahonhunansu, kuma su taka shi da ƙafafuwansu, duk lokacin na ƙarshensu ya wuce a kan shi sai a dawo da na farkonsu. Zai ci gaba akan wannan halin na azaba tsawon yinin alƙiyama wacce gwargwadan yininta shekara dubu hamsin ne, har sai Allah Ya yi hukunci tsakanin halitta, sai ya zama daga 'yan aljanna ko daga 'yan wuta. Na huɗu: Wanda ya mallaki dawakai, su dawakai nau'i uku ne: Na farko: Su laifi ne gare shi, shi ne wanda ya riƙesu dan riya da alfahari da kuma yaƙar ma'abota Musulunci. Na biyu: Su sutura ne gare shi, shi ne wanda ya riƙesu dan yin yaƙi a tafarkin Allah, sannan ya kyautata musu da ciyar da su da ragowar ɗawainiyarsu, daga cikinsu (akwai) barbarar namijinsu. Na uku: Su lada ne gare shi, shi ne wanda ya riƙesu dan yin yaƙi a tafarkin Allah ga ma'abota Musulunci, su a cikin ciyayinsu da dausayinsu dan yin kiwo, to ba abinda zasu ci sai an rubuta masa kyakkyawa adadin abinda suka ci, kuma an rubuta masa kyakkyawa adadin torosonsu da fitsarinsu, ba'a yanke igiyarsu ba, ita ce igiyar da ake ɗauresu a cikinta, suka yi gudu kuma suka yi sukuwa a ƙasa maɗaukakiya; sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa adadin gurabensu da torosonsu, kuma ma'abocinsu bai wuce ba akan wata ƙorama sai su sha daga gareta kuma ba ya nufin ya shayar da su, sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa adadin abinda suka sha . Sannan aka tambayi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi game da jakuna shin su irin dawakai ne? Sai ya ce: Shar'antawa bai sauka ba a sha'aninsu sai dai wannan ayar wacce irinta kadan ne, ita mai gamewa ce ga dukkan nau'ikan ɗa'a da saɓo; ita ce faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Wanda ya aikata kwatankwacin ƙwayar komayya na alheri zai gan shi, wanda yaaikata kwatankwacin ƙwayar komayya na sharri zai ganshi}. [al-Zilzalah: 8], wanda ya yi aiki a cikin mallakar jakai dan yin ɗa'a zai ga ladan hakan, idan kuma ya aikata saɓo to zai ga uƙubar hakan, kuma wannan mai ƙunsar dukkan ayyuka ne.

Fa’idoji
  1. Wajabcin bada zakka, da narko mai tsanani akan hanata.
  2. Rashin kafircin wanda ya hana zakka dan kasala, sai dai cewa shi yana kan haɗari mai tsanani.
  3. Mutum ana ba shi lada akan rabe-raben da suke afkuwa a cikin aikata ɗa'a, idan ya nufi asalinta, koda bai yi nufin waɗancan rabe-raben ba.
  4. Akwai wani haƙƙi a cikin dukiya banda zakka.
  5. Daga haƙƙi a raƙuma (akwai) tatsar nononsu ga wanda ya zo wurinsu cikin miskinai a wurin da zasu sha ruwa; dan ya zama mafi sauƙi ga mabuƙaci daga nufin masaukai, kuma mafi sauƙi ga dabbobin, Ibnu Baɗɗal ya ce: A kwai haƙƙoƙi biyu a cikin dukiya: Farilla ta aini da waninsa, tatsar nonon yana daga haƙƙoƙin da suke daga cikin manyan ɗabi'u.
  6. Daga haƙƙi na wajibi a cikin raƙuma da shanu da tumakai barbarar namijinsu idan an nemi bada aronsa.
  7. Hukuncin jakai da dukkan abinda nassi bai zo da shi ba: Cewa shi mai shiga ne cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Wanda ya aikata kwatankwacin ƙwayar komayya na alheri zai gan shi, wanda ya aikata kwatankwacin ƙwayar komayya na sharri zai gan shi}.
  8. A cikin ayar akwai kwaɗaitarwa a aikata aikin alheri koda kaɗan ne, da tsoratarwa daga aikata sharri ko da ƙasƙantacce ne.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 175) (4962). صحيح مسلم (2/ 680) (987). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين. بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 350). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 862). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 253). تيسير الكريم الرحمن في تفسير كلام المنان، لعبد الرحمن آل سعدي (ص335). فتح الباري شرح صحيح البخاري، لابن حجر (3/ 268). شرح الزرقاني على موطأ مالك، لمحمد الزرقاني (2/ 164). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (4/ 1262).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An gina Musulunci abisa abubuwa biyar

عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ عُمَر رضي الله عنهما قال: قال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: «بُنِيَ الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَحَجِّ الْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ».
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar dabi'un musulunci kamar cika ginin ne, Farkon wadanan rukunan: Shaidawa biyu; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (shaidawa) Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, su rukuni daya ne; dayansu ba ya rabuwa da dayan, bawa zai furtasu yana mai tabbatar da kadaituwar Allah da kuma cancantarSa ga bauta Shi kadai banda waninSa, kuma yana mai aiki da abinda suka hukunta, kuma yana mai imani da Manzancin Annabi Mukammadu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana mai binsa. Rukuni na biyu: Tsaida sallah, su ne sallolin farillai biyar a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da magariba, da Lisha, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu. Rukuni na uku: Fitar da zakkar farilla, ita ibada ce ta dukiya wajiba a kowacce dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga wadanda suka cancanceta. Rukuni na hudu: Hajji, shi ne nufin Makka dan tsaida ibadu, dan yin bauta ga Allah - Mai girma da daukaka -. Rukuni na biyar: Azumin Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga masu bata azimi da niyyar bauta ga Allah, daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana.

Fa’idoji
  1. Lazimtuwar shaidawa biyu, dayansu ba ya inganta sai da dayan; saboda haka ya sanya su rukuni daya ne.
  2. Shaidawa biyu su ne tushen Addini, ba'a karbar wata magana ko wani aiki sai da su.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 11) (8)، صحيح مسلم (1/ 45) (16)، و(1/ 88) (82)، فتح الباري لابن رجب (1/ 22)، جامع العلوم والحكم (1/147)، شرح الأربعين لابن العطّار (ص 62)، شرح الأربعين النووية لعبد الكريم الخضير (ص 87)، فتح القوي المتين في شرح الأربعين للعباد (ص 29)، شرح الأربعين النووية لصالح آل الشيخ (ص 91 - 95)، التحفة الربانية لإسماعيل الأنصاري (ص 12).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar

عن أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ رضي الله عنه قال: بينما نحن جلوس مع النبي صلى الله عليه وسلم في المسجد دخل رجل على جمل، فأناخه في المسجد ثم عقله، ثم قال لهم: أيكم محمد؟ والنبي صلى الله عليه وسلم متكئ بين ظهرانيهم، فقلنا: هذا الرجل الأبيض المتكئ. فقال له الرجل: يا ابن عبد المطلب فقال له النبي صلى الله عليه وسلم: «قد أجبتك». فقال الرجل للنبي صلى الله عليه وسلم: إني سائلك فمشدد عليك في المسألة، فلا تجد علي في نفسك؟ فقال: «سل عما بدا لك» فقال: أسألك بربك ورب من قبلك، آلله أرسلك إلى الناس كلهم؟ فقال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصلي الصلوات الخمس في اليوم والليلة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصوم هذا الشهر من السنة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن تأخذ هذه الصدقة من أغنيائنا فتقسمها على فقرائنا؟ فقال النبي صلى الله عليه وسلم: «اللهم نعم». فقال الرجل: آمنت بما جئت به، وأنا رسول من ورائي من قومي، وأنا ضمام بن ثعلبة أخو بني سعد بن بكر.
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Anas dan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa: Lokacin da sahabbai suna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci yayin da wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya durkusar da rakumin sannan ya daure shi. Sannan ya tambayesu: Waye Muhammd a cikinku? Alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide tsakanin mutanen, sai muka ce : Wannan farin mutumin. Sai mutumin ya ce da shi: Yakai Dan Abdul Muddalib. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: Na ji ka yi tambaya in amsa maka. Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne kuma mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji wani abu game dani a ranka. Wato: Kada ka yi fushi da ni kuma kada kunci ya sameka. Sai ya ce: Ka tambayi abinda kake so. Sai ya ce: Ina ina hada ka da Ubangijinka kuma Ubangijin wadanda suka gabace ka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane? Sai ya ce: Eh ya Allah, dan karfafa gaskiyarsa. Sai Mutumin ya ce: Ina yi maka magiya da Allah, wato; Ina tambayarka sabo da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka yi salloli biyar a yini da dare? Su ne salloli wadanda aka faralanta ?., Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu azimci wannan watan daga shekara? wato: Watan Ramadan, Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka daka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawanmu? ita ce zakka. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Eh ya Allah, Sai Dimam ya musulunta, kuma ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa shi zai kira mutanensa zuwa Musulunci. Sannan ya yi bayanin kansa cewa shi ne Dimam dan Sa'alabata daga Banu Sa'ad Ibnu Bakar.

Fa’idoji
  1. Tawali'un Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -; dan mutum ba zai iya banbancewa ya raba tsakaninsa da sahabbansa ba.
  2. Kyakkyawar dabi'un Annabi - aminci ya tabbata agare shi -, da tausasawarsa a bada amsa ga mai tambaya, kuma cewa kyakkyawar bada amsa tana daga sabubban karbar Da’awah.
  3. Halaccin bayanin mutum da wata siffa na fari da ja, da tsawo da gajarta, da makamancin wannan daga abinda ba'a nufin aibatawa da shi, idan ba ya kin hakan.
  4. Halaccin shigar kafiri masallaci dan bukata.
  5. Bai ambaci Hjji ba a cikin hadisin domin cewa shi zai iya kasancewa ba'a wajabta Hajjin ba a lokacin zuwansa ba.
  6. Kwadayin sahabbai akan kiran mutane; daga musuluntarsa ya yi kwadayin kiran mutanensa.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 23) (63)، صحيح مسلم (1/ 41) (12)، شرح ابن بطال (1/145)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (2/ 22).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An gina Musulunci abisa abubuwa biyar

عَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «بُنِيَ الإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لَا إلَهَ إلَّا اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا ‌عَبْدُهُ ‌وَرَسُولُهُ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَحَجِّ الْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ».
Daga Abu Abdurrahman Abdullahi ibnu Umar ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar dabi'un musulunci kamar cika ginin ne, Farkon wadanan rukunan: Shaidawa biyu; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (shaidawa) Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, su rukuni daya ne; dayansu ba ya rabuwa da dayan, bawa zai furtasu yana mai tabbatar da kadaituwar Allah da kuma cancantarSa ga bauta Shi kadai banda waninSa, kuma yana mai aiki da abinda suka hukunta, kuma yana mai imani da Manzancin Annabi Mukammadu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana mai binsa. Rukuni na biyu: Tsaida sallah, su ne sallolin farillai biyar a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da magariba, da Lisha, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu. Rukuni na uku: Fitar da zakkar farilla, ita ibada ce ta dukiya wajiba a kowacce dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga wadanda suka cancanceta. Rukuni na hudu: Hajji, shi ne nufin Makka dan tsaida ibadu, dan yin bauta ga Allah - Mai girma da daukaka -. Rukuni na biyar: Azumin Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga masu bata azimi da niyyar bauta ga Allah, daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana.

Fa’idoji
  1. Lazimtuwar shaidawa biyu, dayansu ba ya inganta sai da dayan; saboda haka ya sanya su rukuni daya ne.
  2. Shaidawa biyu su ne tushen Addini, ba'a karbar wata magana ko wani aiki sai da su.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 11) (8). صحيح مسلم (1/ 45) (16)، و(1/ 88) (82). فتح الباري لابن رجب (1/ 22). جامع العلوم والحكم (1/147). شرح الأربعين لابن العطّار (ص 62). شرح الأربعين النووية لعبد الكريم الخضير (ص 87). فتح القوي المتين في شرح الأربعين للعباد (ص 29). شرح الأربعين النووية لصالح آل الشيخ (ص 91 - 95). التحفة الربانية لإسماعيل الأنصاري (ص 12).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com