Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai Rana da Wata ayoyi ne daga cikin ayoyoin Allah, wanda yakan tsoratar da bayinsa da su,kuma lallai ba su kisifewa don mutuwar wani da ga cikin mutane- don haka in kun ga wani abu makamancin hakan to ku yi sallah, ku roki Allah har ya yaye muku

عن أبي مسعود عُقبة بن عَمْرو الأنصاري البَدْري رضي الله عنه مرفوعاً: «إن الشمس والقمر آيتان من آيات الله، يُخَوِّفُ الله بهما عباده، وإنهما لا يَنْخَسِفَان لموت أحد من الناس، فإذا رأيتم منها شيئا فَصَلُّوا، وَادْعُوا حتى ينكشف ما بكم»
Lallai Rana da Wata ayoyi ne daga cikin ayoyoin Allah, wanda yakan tsoratar da bayinsa da su, kuma lallai ba su kisifewa don mutuwar wani da ga cikin mutane- don haka in kun ga wani abu makamancin hakan to ku yi sallah, ku roki Allah har ya yaye muku
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzo mai tsira da aminci ya bayyana cewa Rana da Wata suna daga cikin ayoyin Allah masu nuni akan kudurar Allah da hikimarsa, canjawarsu daga asalin yadda suke baya faruwa don rayuwa ko mutuwar wasu manyan mutane kamar yadda mutanen jahiliyya suke kudurcewa,abubuwanda kan afku a duniya basu da tasiri a kansu. kisifewar Rana ko Wata kan faru ne saboda tsoratar da bayi, don zunubansu haka kuma don su sabunta tubansu, don kuma su koma zuwa ga Allah Madaukaki. Don haka Manzo ya shiryar akan a tashi ayi salla da addu'a har su sami waraka su yaye. lallai ga Allah sururruka da jujjuyawar al'amura suke

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426ه عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 ه صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SALLAR ZAZZAƁIN RANA DA NA WATA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com