Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SALLAR IDI BIYU

Hadisai 2

Annabi ya kasance -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- da Abubakar da Umar sunayin Sallar Idi kafin Huduba

عن عبد الله بن عُمر رضي الله عنهما قال: «كان النبي صلى الله عليه وسلم وأبو بكر وعُمر يصلون العيدين قبل الخُطْبة».
Daga Abdullahi Dan Umar -Allah ya yarda da su- ya ce: "Annabi ya kasance -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- da Abubakar da Umar sunayin Sallar Idi kafin Huduba"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Yakasance yana daga Al'adar Annabi da Halifofinsa, cewa sunayin Sallar Idi da Mutane, a karamar sallah da Babba, kuma suyi Huduba kuma su fara Sallah kafin Huduba, kuma hakan yaci gaba da faruwa har zuwan Marwan shi ne yayi Huduba kafin Sallah

Madogara

تيسير العلام، للبسام، الناشر: مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة العاشرة، 1426هـ - 2006م. تنبيه الأفهام، للعثيمين، طبعة مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة الأولى، 1426هـ. صحيح البخاري، لأبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر، الناشر: دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. صحيح مسلم، لأبي الحسين مسلم بن الحجاج القشيري، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. تأسيس الأحكام، لأحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، القاهرة، مصر، الطبعة الأولى.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- ya umarce mu da mu fito sallar idi guda biyu yara mata da suka fara wayo da `yan matan da ake tsarewa cikin dakuna a cikin gidaje, ya kuma umarci mata masu haila da su nisaci wuraren sallah na musulmi

عن أم عَطيَّة نُسَيْبة الأنصارية رضي الله عنها قالت: «أَمَرَنا رسول الله صلى الله عليه وسلم أن نُخْرِج في العيدين الْعَوَاتِقَ وَذَوَاتِ الْخُدُورِ، وأَمَر الحُيَّض أن يَعْتَزِلْنَ مُصلّى المسلمين». وفي لفظ: «كنا نُؤمر أن نَخْرُجَ يوم العيد، حتى نُخْرِجَ الْبِكْرَ من خِدْرِهَا، حَتَّى تخرجَ الْحُيَّضُ، فَيُكَبِّرْنَ بتكبيرهم ويدعون بدعائهم، يرجون بَرَكَة ذلك اليوم وطُهْرَتَهُ».
An karbo daga Ummu atiyyah ita ce Nusaibah mutuniyar madina Allah ya kara yadda a gareta ta ce:{manzon Allah tsira da aminci su kara tabbata a gareshi- ya umarcemu da mu fito sallae idi guda biyu yara mata da suka fara wayo da `yan matan da ake tsarewa cikin dakuna a cikin gidaje, ya kuma umarci mata masu haila da su nisaci wuraren sallah na musulmi}. a wani lafazin kuma: {Mun kasance ana umartar mu da mu fito ranar idi, harma mufito da `yan mata daga cikin dakunan su, har da masu haila ma su fito, sai suyi kabbara tare da kabbarar masu sallah suyi addu`ah da addu`ar su, suna masu fatan samun albarkar wannan yini da tsarkins}.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ranar idin karamar sallah da ranar idin babbar sallah na daga cikin ranaku masu falala, wadanda alamomin musulunci ke bayyana a cikinsu`yan`uwantakar musulmi tana bayyana a fili ta hanyar haduwar su waje daya da tattaruwar su a sahu-sahu, dukkan mutanen gari suna tattaruwa a waje guda don bayyanar da hadin kan su, da haduwar zukatan su, da haduwar kalmar su bisa taimakon addinin musulunci, da daukaka kalmar Allah tare da tsaida ambaton Allah da bayyanar da alamominsa. saboda haka ne annabi mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi yayi umarni da a fitowar dukkan mata, harma da dukkan `yan matan da aka suturce su cikin gidajen su fitowar tana kansu, da mata masu jinin haila, saidai zasu zauna ne a nesa da masu sallah, domin su halarci alheri da addu`ar musulmai sai su samu alheran wannan taro, su kuma samu albarka sa, da samun rahamar Allah da yardar sa don rahamar ta kasance da samun karbuwa ta zamo mafi kusa garesu. sallar idi guda biyu farilla ce ta kifaya.

Madogara

تيسير العلام، للبسام، الناشر: مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة العاشرة، 1426هـ - 2006 م. تنبيه الأفهام، للعثيمين، طبعة مكتبة الصحابة، الامارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة الأولى 1426هـ. صحيح البخاري، لأبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري.، تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر، الناشر: دار طوق النجاة، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com