Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ka yi Sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki

عن عمران بن حصين رضي الله عنه قال: كَانَتْ بِي بَوَاسِيرُ، فَسَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الصَّلَاةِ، فَقَالَ: «صَلِّ قَائِمًا، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَقَاعِدًا، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَعَلَى جَنْبٍ».
Daga Imaran Ɗan Husain Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na kasance Ina da basir, sai na tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da sallah sai ya ce: Ka yi Sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana asali a Sallah shi ne a yi ta a tsaye, sai idan ba za a iya ba, sai a yi ta a zaune, idan ba zai iya sallar a zaune ba, to, ya samu ya yi a gefen jikinsa.

Fa’idoji
  1. Sallah ba ta faɗuwa muddin hankali na nan, sai ya kasance daga wannan yanayin, zuwa wancan yanayin gwargwadon damar da yake da ita.
  2. Sauƙi da rangwamen Musulunci cewa bawa zai aikata ibada yadda yake da iko.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 48) (1117). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبدالله البسام (2/ 322). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (3/ 202).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SALLAR MASU UZURI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com