Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kuma ai ansanya Limami ne don ayi koyi da shi, to kuma kada ku saba Masa, to idan yayi kabbara to kuyi kabbara, kuma idan yayi ruku'u to kuyi ruku'i, kuma idan yace Allah yaji mai gode masa,to ku ce: Ubangijinmu godiya ta tabbata a gareka, kuma idan yayi Sujada to kuyi Sujada, kuma idan yai Sallah a zaune to kuyi sallah kuma a a zaune baki dayanku

عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «إنما جُعِلَ الإمام ليِؤُتَمَّ به، فلا تختلفوا عليه، فإذا كبر فكبروا، وإذا ركع فاركعوا، وإذا قال: سمع الله لمن حمده، فقولوا: ربنا ولك الحمد. وإذا سجد فاسجدوا، وإذا صلى جالسا فصلوا جلوسا أجمعون».
Daga Abu Huraira -Allah yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Kuma ai ansanya Limami ne don ayi koyi da shi, to kuma kada ku saba Masa, to idan yayi kabbara to kuyi kabbara, kuma idan yayi ruku'u to kuyi ruku'i, kuma idan yace Allah yaji mai gode masa,to ku ce: Ubangijinmu godiya ta tabbata a gareka, kuma idan yayi Sujada to kuyi Sujada, kuma idan yai Sallah a zaune to kuyi sallah kuma a a zaune baki dayanku"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi ya shiryar da mamu izuwa Hikimar da ta sa aka sanya Limami kuma ita ce cewa duk wanda ya bishi Sallah to yayi koyi da shi a Sallarsa, kuma kada ya saba Masa da wani aiki na ayyukan Sallah, kuma ya kula da duk motsinsa a tsare to idan yai kabbarar harama, to kuyi harama kuma, kuma idan yayi ruku'u to kuyi ruku'i bayansa, kuma idan ya tunasar da ku cewa Allah yana amsa fadin wanda ya gode masa to ku godewa Allah da fadinku, kuma wata sigar ta zo daban kamar ya Ubangiji Ubangijinmu godiya a gareka, kuma idan yayi sujada to ku bishi kuma kuyi sujad, kuma idan yai sallah a zaune -sabida gajiyawa ga barin iya tsayiw- to sabida tabbatar da biyayya kuma kuyi sallah a zaune kuma koda zaku iya tsayiwa.

Madogara

- صحيح البخاري، للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب، الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام، للشيخ إسماعيل الأنصاري -مطبعة السعادة- الطبعة الثانية، 1392ه. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام، تحقيق محمد صبحي حسن حلاق، مكتبة الصحابة، الشارقة، الطبعة العاشرة، 1426ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HUKUNCE-HUKUNCEN LIMAN DA MAMU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com