Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أَمَا يَخْشَى أَحَدُكُمْ - أَوْ: لاَ يَخْشَى أَحَدُكُمْ - إِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ قَبْلَ الإِمَامِ، أَنْ يَجْعَلَ اللَّهُ رَأْسَهُ رَأْسَ حِمَارٍ، أَوْ يَجْعَلَ اللَّهُ صُورَتَهُ صُورَةَ حِمَارٍ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana narko mai tsanani akan wanda ya dago kansa kafin limaminsa, Allah Ya maida kansa kan jaki, ko Ya maida surar halittarsa ta zama surar jaki.

Fa’idoji
  1. Akwai halaye hudu ga mamu tare da liman: Uku an hana, su ne: Rigayarsa da daidai da shi da jinkirta masa. Abinda ya halatta ga mamu: Bin liman.
  2. Wajabcin mamu ya bi liman a sallah.
  3. Narko da canja surar wanda yake dago kansa kafin liman zuwa surar jaki abu ne mai yiwuwa, shi ne shafewa.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 140) (691). صحيح مسلم (1/ 321) (427). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 111). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص65). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص133).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HUKUNCE-HUKUNCEN LIMAN DA MAMU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com