Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan an tsaida sallah to babu wata sallah sai ta farilla kawai

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صلَّى اللَّهُ عليْه وسلَّمَ، قَالَ: «إِذَا أُقِيمَتِ الصَّلَاةُ فَلَا صَلَاةَ إلَّا المَكْتُوبَةُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Idan an tsaida sallah to babu wata sallah sai ta farilla kawai».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda yake cikin masallaci ya fara yin sallar nafila bayan an yi iƙamar sallar farilla.

Fa’idoji
  1. Hani daga yin sallar nafila idan an yi iƙamar sallar farilla alhali shi yana cikin masallaci.
  2. Hani akan fara nafila bayan an yi iƙamar sallah, daidai ne ta kasance ratiba ce kamar sunnar Asuba da Azahar ko waninta.
  3. Idan an yi iƙamar sallah alhali shi yana yin nafila; idan mafi ƙaranci daga raka'a ya rage to ya cikata a sauƙaƙe, inba haka ba to sai ya yanketa har ya riski falalar kabbarar harama.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 493) (710). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (15/ 246).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR SALLAR JAM'I DA HUKUNCE-HUKUNCENTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com