Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya zo masallaci dan yin ibada ko ilimi ko wanin hakan daga manufofin alheri a kowanne lokaci albishir; a farkon yini ko ƙarshensa da cewa Allah haƙiƙa ya tanadar masa da wani wuri da garar baƙi a cikin aljanna, duk lokacin da ya zo masallaci a dare ko yini.
Fa’idoji
Falalar tafiya zuwa masallaci, da kwaɗaitarwa akan kiyayewa akan yin sallar jam'i a cikinsa, da yawa mai ƙin zuwa masallaci alheri da falala da lada da garar baƙi suke wuce shi waɗanda Allah - alherinSa ya yawaita Ya ɗaukaka - ga masu nufin ɗakinSa.
Idan mutane sun kasance suna girmama wanda ya zo gidajensu, suna gabato masa da abinci, to Allah - alherinSa ya yawaita Ya ɗaukaka - Shi ne Mafi kyauta daga halittarSa! wanda ya nufi ɗakinSa zai girmama shi, kuma Allah Zai tanadar masa da masauki mai girma kuma babba.
Farin ciki da nishaɗi da tafiya masallatai; domin ana tanadar masa da masauki a duk lokacin ya wayi gari ko ya kai maraice da adadin tafiyarsa.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 133) (662).
صحيح مسلم (1/ 463) (669).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 153).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 166).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 204).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com