Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba

عَن أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «تَفْضُلُ صَلاَةُ الجَمِيعِ صَلاَةَ أَحَدِكُمْ وَحْدَهُ، بِخَمْسٍ وَعِشْرِينَ جُزْءًا، وَتَجْتَمِعُ مَلاَئِكَةُ اللَّيْلِ وَمَلاَئِكَةُ النَّهَارِ فِي صَلاَةِ الفَجْرِ» ثُمَّ يَقُولُ أَبُو هُرَيْرَةَ: فَاقْرَءُوا إِنْ شِئْتُمْ: {إِنَّ قُرْآنَ الفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا} [الإسراء: 78].
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba" Sannan Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartowar (mala'iku) ne} [al-Isra'i: 78].
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa lada da sakamakon sallar mutum a cikin jama'a tare da liman ya fi sallah ashirin da biyar da mutum zai sallace su shi kaɗai a cikin gidansa ko kasuwarsa, sannan (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa mala'ikun dare da rana suna taruwa a sallar Asuba, sannan Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce yana mai kafa hujja akan hakan: Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartar (mala'iku) ne} [al-Isra'a: 78]. Wato: Lallai sallar Asuba mala'ikun dare da mala'ikun rana suna halartarta.

Fa’idoji
  1. Ibnu Hajar ya ce: Lallai sallah a cikin masallaci a jam'i tana ƙaruwa akan sallah a cikin gida da cikin kasuwa a jam'i da ɗaiɗaiku, Ibnu Daƙiƙul Eid ma ya faɗi hakan.
  2. A cikinsa akwai falalar sallar Asuba; dan keɓantuwar mala'iku da ita.
  3. Ibnu Baaz ya ce: Yana kamata ga mumini ya yi kwaɗayin kiyaye sallah a cikin jama'a koda gidansa ya yi nisa dan ya samu wannan alherin mai girma.
  4. Nawawi ya faɗa a akan haɗa wadannan ruwayoyin cewa sallar jama'a ta fi sallar mutum ɗaya da daraja ashirin da biyar, ɗaya riwayar kuma da ashirin da bakwai: Haɗawa tsakaninsu ta fuskoki uku ne: Ta farkonsu: Cewa babu korewa (tsakaninsu), ambatan kaɗan ba ya kore mai yawa, kuma mafhumul adadi ɓatacce ne a wurin malaman Usulul Fiƙhi. Na biyu: Ta zama tun farko ya labarta kaɗan ɗin, sannan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanar da shi ƙarin falala, sai ya bayar da bayaninta. Na uku: Cewa shi ya banbanta a tsakanin yanayin masallata da kuma sallar, sai ta zama ashirin da biyar ga wasunsu, ga wasunsu kuma ashirin da bakwai gwargwadan cikar sallar da kuma kiyayewarsa akan siffarta da kushu'inta da yawan jama'arta da falalarsu da kuma darajar wurin (sallar) da makamancin hakan. Allah ne Mafi sani.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 131) (648). صحيح مسلم (1/ 450) (649). تيسير الكريم الرحمن في تفسير كلام المنان، لعبد الرحمن آل سعدي (ص464). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 210).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR SALLAR JAM'I DA HUKUNCE-HUKUNCENTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com