Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SHARUƊAN SALLAH

Hadisai 24

Yayin da mutane suke tsaye a sallar asuba yayin da suka zo, yana zuwa, sai ya ce: An saukar da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a gare shi a daren yau kuma an saukar da Alkur'ani, kuma an kira su su karbe shi, kuma sun karbe shi

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: «بَينَمَا النَّاس بِقُبَاء في صَلاَة الصُّبحِ إِذْ جَاءَهُم آتٍ، فقال: إِنَّ النبِيَّ صلى الله عليه وسلم قد أُنزِل عليه اللَّيلةّ قرآن، وقد أُمِرَ أن يَستَقبِل القِبْلَة، فَاسْتَقْبِلُوهَا، وكانت وُجُوهُهُم إلى الشَّام، فَاسْتَدَارُوا إِلى الكَّعبَة».
A kan Abdullah bn Omar - Allah ya yarda da su duka - ya ce: "Yayin da mutane suke tsaye a sallar asuba yayin da suka zo, yana zuwa, sai ya ce: An saukar da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a gare shi a daren yau kuma an saukar da Alkur'ani, kuma an kira su su karbe shi, kuma sun karbe shi. Al-Sham, don haka suka juya zuwa Ka'aba.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ. تنبيه الأفهام، للعثيمين -طبعة مكتبة الصحابة الامارات -مكتبة التابعين- القاهرة- الطبعة الأولى 1426هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida, da Usama Dan Zaidu da Bilal da Usman Dan Dalha

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: «دخل رسول الله صلى الله عليه وسلم البيت، وأسامة بن زيد وبلال وعثمان بن طلحة، فأغلقوا عليهم الباب فلما فتحوا كنت أولَ من وَلَجَ. فلقيتُ بلالًا، فسألته: هل صلى فيه رسول الله صلى الله عليه وسلم ؟ قال: نعم ، بين العَمُودَيْنِ اليَمَانِيَيْنِ».
Daga Abdullah Dan Umar -Allah ya yarda dasu- zuwa ga Annabi: Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida,da Usama Dan Zaidu da Bilal da Usman Dan Dalha sai aka rufe musu kofar, bayan an bude: sai na zama farkon wanda ya shiga, na gamu da Bilal, sai na tambaye shi: shin Manzo tsira da aminci ya yi salla? sai yace e,ya yi tsakanin ginshikai guda biyu
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Lokacin da Allah madaukaki ya bude makha, ya tsarkake dakinsa daga gumaka da butunbutumai da hotuna, sai tsira da aminci ya shiga Dakin Ka'abaa madaukakiya, a tare da shi akwai mai yi masa hidima, Bilal da Usama,da mai kula da gida Usman Dan Dalha,sai aka kulle musu kofa don kada mutane su yi cincirindo wajen shigowar Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi,don su ga ydda yake yin bauta, gudun kar su shagaltar da shi daga abin da yake son yi a wajen,shi ne ganawa da Ubangijinsa tare da gode masa bisa ni'imominsa, yayin da suka jima suna jira , sai aka bude kofar.Abdullahi Dan Umar ya kasance mai tsananin kwadayin bibiyar Sunnar Annabi ne don haka ya zama farkon wanda ya shiga bayan an bude kofar.Sai ya tambayi Bilal : shin Annabi ya yi salla anan ciki ne? sai Boilal yace: e, ya yi salla a tsakanin ginshikan can na bangaren dama .a lokacin Ka'aba Mai tsarki tana da ginshikai shida ne,sai ya sanya uku a bayansa,biyu a damansa daya kuma a hagunsa, kuma ya bar tazara kamu uku tsakaninsa da katanga, sai sallaci raka'a biyu, kuma ya yi addu'a abangarori hudu.

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Manzon Allah, Banyi Sallar La'asar ba har rana ta kusa faduwa, sai Annabi ya ce: "na rantse da Allah ban sallace ta ba, sai muka tashi zuwa Buthan, sai yayi Alwala don yin Sallah, Muma mukai Alwala don yin haka, sai mukai Sallah La'asar bayan rana ta fadi, sannan yai sallar Magariba bayan ta.

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما «أنَّ عمر بن الخَطَاب رضي الله عنه جاء يَومَ الخَندَقِ بَعدَ مَا غَرَبَت الشَّمسُ فَجَعَل يَسُبُّ كُفَّار قُرَيشٍ، وقال: يا رسول الله، مَا كِدتُّ أُصَلِّي العَصرَ حَتَّى كَادَت الشَّمسُ تَغرُبُ، فَقَال النَبِيُّ صلى الله عليه وسلم : والله مَا صَلَّيتُهَا، قال: فَقُمنَا إلَى بُطحَان، فَتَوَضَّأ للصَّلاَة، وتَوَضَأنَا لَهَا، فَصَلَّى العَصر بعد مَا غَرَبَت الشَّمسُ، ثُمَّ صَلَّى بعدَها المَغرِب».
Daga Jabir Dan Abdullahi -Allah ya yarda da shi- "Cewa Umar Dan Khattab -Allah ya yarda da shi- ya zo Ranar Khadak bai rana ta fadi, sai ya fara zagin Kafiran kuraishawa, kuma ya ce: Ya Manzon Allah, Ya Manzon Allah, Banyi Sallar La'asar ba har rana ta kusa faduwa, sai Annabi ya ce: "na rantse da Allah ban sallace ta ba, sai muka tashi zuwa Buthan, sai yayi Alwala don yin Sallah, Muma mukai Alwala don yin haka, sai mukai Sallah La'asar bayan rana ta fadi, sannan yai sallar Magariba bayan ta fadi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Umar Allah ya yarda da shi y zo wajen Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Ranar yakin Gwalalo bayan faduwar Rana yana la'antar kafiran Kuraishawa; saboda sun shagaltar da shi daga yin Sallar La'asar don bai sami yinta ba har Rana ta kusan faduwa, sai Annabi tsira da anminci ya rantse cewa shima bai yi sallar ba har yanzu -Annabi kuwa shi ne Mai gaskiya- Annabi ya yi haka ne don Umar ya sami nutsuwa game da lamarin da ya dame shi. Sannan sai ya mike ya yi alwalla Sahabbai ma suka yi alwalla, sai ya sallaci La'asar sannan ya sallaci Magariba.

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى، 1381هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة، 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم، لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية، 1408هـ. صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Annabi tsira da amincin Allah ya kasance yana yin sallar Azahar a lokacin garjin rana, yakan sallaci La'asar lokaci da rana ta yi garau, Magariba kuma in rana ta fadi

عن جابر بن عبد الله الأنصاري رضي الله عنهما قال: «كَانَ صلى الله عليه وسلم يُصَلِّي الظُّهْرَ بِالهَاجِرَة، والعَصرَ والشَّمسُ نَقِيَّة، والمَغرِب إِذَا وَجَبَت، والعِشَاء أَحيَانًا وأَحيَانًا: إِذَا رَآهُم اجتَمَعُوا عَجَّل، وَإِذَا رَآهُم أَبْطَئُوا أًخَّر، والصُّبحُ كان النبي صلى الله عليه وسلم يُصَلِّيهَا بِغَلَس».
Daga Jabir Dan Abdullah mutumin Madina -Allah ya yarda da su- yace: "Annabi tsira da amincin Allah ya kasance yana yin sallar Azahar a lokacin garjin rana, yakan sallaci La'asar lokaci da rana ta yi garau, Magariba kuma in rana ta fadi, Issha'i kuma wani lokacin ya ggaggauta yinta in ya ga an taru, wani likacin kuma ya jinkirta ta in yaga an makara, Asuba kuma ya kasance yana yin ta da sauran duhu"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wannan hadisi yana nuni da lokacin da yafi a yi kowacce daga cikin salloli biyar,ka ga sallar Azahar:ana yin tane lokacin da rana ta karkata daga tsakkiya,shi ne lokacin zawali, shi ne farkon lokacinta.La'a sar kuma: ana yinta lokacin da rana take fara fat, ba wani fatsi-fatsi da ya gauraya da ita,yadda ake gane lokacinta shi ne tsawon komai ya lunka, Magariba kuma ana yinta ne lokacin faduwar rana da sanda ta buya. Issha'i kuma sai a kula da yanayin mutane in sun zo da wuri a farkon lokacinta,shi ne lokacin buyan jan shafaki to sai a yi ta, in kuma basu zo ba to sai a jinkirta ta har wajen tsakkiyar dare na farko, don shi ne lokacinta da ya fi ba don takurawa ba. amma Asuba shi ne farkon lokacin da haske ya fara dan bullowa

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ. الإفهام في شرح عمدة الأحكام لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، ط1، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، 1434هـ. تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ. شرح العمدة للسعدي، قيده عنه تلميذه: عبد الله العوهلي، تقديم: عبد الله بن عبد العزيز العقيل، تحقيق: أنس بن عبد الرحمن بن عبد الله العقيل، ط1، دار التوحيد، الرياض، 1431هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ananbi tsira da amincin Allah ya yi dare bai fito sallar Issha'i ba, sai Umar ya fito yace: salla ya Manzon Allah mata da yara sun yi bacci, sai Manzo ya fito kansa yana digar da ruwa yana cewa: ba don kar in takurawa al'ummata ba, da na umarce su da yin wannan sallar a irin wannan lokacin.

عن عَبْد اللَّهِ بْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قال: «أّعْتَمَ النَبِيُّ -صلَّى الله عليه وسلَّم- بِالعِشَاء، فَخَرَج عُمَر فقال: الصَّلاةَ يا رسول الله، رَقَد النِسَاءُ والصِّبيَان. فَخَرَجَ ورَأسُهُ يَقطُر يقول: لَولاَ أن أَشُقَّ عَلَى أُمَّتِي -أو على النَّاس- لَأَمَرتُهُم بهذه الصَّلاة هذه السَّاعَة».
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi: "Annabi tsira da amincin Allah ya yi dare bai fito sallar Issha'i ba,siai Umar ya fito yace: salla ya Manzon Allah mata da yara sun yi bacci,sai Manzo ya fito kansa yana digar da ruwa yana cewa: ba don kar in takurawa al'ummata ba, da na umarce su da yin wannan sallar a irin wannan lokaci
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi ya jinkirta fitowa zuwa ga sallar issha'i har dare yayi ,mata da yara sun kwanta bacci,wanda basu da jumurin jira mai tsawo,sai Umar Dan Khaddab ya zo wajensa yace: sallah,mata da yara sun yi bacci. sai Manzo tsira da aminci ya fito daga gidansa zuwa masallaci kansa yana digar da ruwan wanka yana bayyana cewa mafi kyawun liokacin sallar issha'i shine a jinkirta ta.ba don gudun wahalar jiran lokacin ba:ba don kan in matsawa al'umma ta ba da na umarce su da wannan sallar a irin wannan lokacin

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah tsira da amincin Allah ya kasance yana sallar Asuba, Muminai mata suna zuwa lullube da mayafansu, sannan su koma gidajensu ba wanda ke gane su, saboda sauran duhun dare.

عن عَائِشَة رضي الله عنها قالت: (لقد كان رسولُ الله صلى الله عليه وسلم يُصَلِّي الفَجر، فَيَشهَدُ معه نِسَاء مِن المُؤمِنَات، مُتَلَفِّعَاتٍ بِمُرُوطِهِنَّ، ثم يَرجِعْن إلى بُيُوتِهِنَّ مَا يُعْرِفُهُنَّ أحدٌ من الغَلَس).
Daga Aisha -Allah ya yarda da ita- tace: (Manzon Allah tsira da amincin Allah ya kasance yana sallar Asuba, Muminai mata suna zuwa lullube da mayafansu, sannan su koma gidajensu ba wanda ke gane su, saboda sauran duhun dare
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Aisha -Allah ya yarda da ita tana ambata mana cewa: Matan Sahabbai sun kasance suna lullube jikinsu da tufafinsu kuma su je sallar Asuba tare da Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, kuma har su koma gidajensu ba mai gane su, duk da kasancewar haske ya dan fara bayyana, tare da sauran duhun. Littafin Taisiril Ahkam, na Malam Bassam, shafi na 86

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408هـ. صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na yi barci a hannun Manzon Allah - SAW- kuma kafafuna suna cikin sumbatansa, don haka lokacin da ya yi sujada, sai ya damke ni, sai kafafuna suka dafe

عن عائشة رضي الله عنها قالت: «كنت أنام بين يَدَيْ رسول الله صلى الله عليه وسلم ورِجْلايَ فِي قِبْلَتِهِ، فإذا سجد غَمَزَنِي، فقَبَضتُ رِجْلَيَّ، فإذا قام بَسَطْتُهُمَا، والبيوت يومئذ ليس فيها مصابيح».
Daga A’isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: “Na yi barci a hannun Manzon Allah - SAW- kuma kafafuna suna cikin sumbatansa, don haka lokacin da ya yi sujada, sai ya damke ni, sai kafafuna suka dafe.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

تيسير العلام، للبسام، الناشر: مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة العاشرة، 1426هـ - 2006 م. تنبيه الأفهام، للعثيمين، طبعة مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة الأولى 1426هـ. الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لعبد العزيز بن باز، اعتناء سعيد بن علي بن وهف القحطاني، الرياض، الطبعة الأولى 1435هـ. الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري، طبعة دار الفكر، دمشق، الطبعة الأولى 1381هـ. خلاصة الكلام، فيصل المبارك الحريملي، الطبعة الثانية، 1412 هـ - 1992م. صحيح البخاري، لأبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر، الناشر: دار طوق النجاة، الطبعة الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، لأبي الحسين مسلم بن الحجاج النيسابوري، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na shiga ni da Mahaifina ga Abu Baraza Al-aslami, sai Mahaifina ya ce da shi:yaya Annabi SAW yake sallar farilla?

عن أبي المنهال سيار بن سلامة قال: (دَخَلتُ أنا وأبي علَى أبي بَرزَة الأسلمي، فقال له أبي: كيف كان النبي صلى الله عليه وسلم يصلي المَكْتُوبَة؟ فقال: كان يُصَلِّي الهَجِير -التي تدعونها الأولى- حِينَ تَدحَضُ الشَّمسُ. ويُصَلِّي العَصرَ ثم يَرجِعُ أَحَدُنَا إلى رَحلِه في أَقصَى المدينة والشَّمسُ حَيَّة، ونَسِيتُ ما قال في المَغرب. وكان يَسْتَحِبُّ أن يُؤَخِّر من العِشَاء التي تَدعُونَها العَتَمَة، وكان يَكرَه النَّوم قَبلَهَا، والحديث بَعدَها. وكان يَنْفَتِلُ من صَلَاة الغَدَاة حِين يَعرِفُ الرَّجُل جَلِيسَه، وكان يَقرَأ بِالسِتِّين إلى المائة).
An rawaito daga Al-minhal Sayar Bn Salama ya ce: (Na shiga ni da Babana ga Abu baraza Al-aslami, sai ya ce da shi yaya Annabi SAW yake Sallar farilla? sai ya ce: ya Kasance yana Sallar Azahar -wacce suke kiranta ta farko- lokacin da Rana ta karya, kuma yana Sallatar La'asar sannan dayan mu ya dawo zuwa Masaukinsa a karshen Madina Rana tana nan, na manta abunda ya ce a Magriba, kuma ya Kasance yana son ya jinkirta Isha wacce muke kiranta Al-atama, kuma ya kasance yana kin ayi bacci kafinta, da kuma yin Magana Bayanta kuma ya kasance yana yana tafiya daga Sallar Asuba lokacin da Mutum zai iya gane na kusa da shi, kuma ya kasance yana Karanta Aya Sttin zuwa Dari.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abu Barzah -Allah ya yarda da shi- ya fadi lokutan Sallar Farilla, Sai ya fara da cewa shi Annabi SAW ya Kasance yana Sallar Azahar, lokacin da Rana ta Karkata daga daga tsakiyar Sama zuwa Yamma, kuma wannan shi ne farkon lokacinta, kuma yana Sallar La'asar, sannan daya daga Masallatan ya dawo gidan sa a mafi nisan wuri daga Madina kuma Rana bata gushe ba tana nan, wannan shi ne farkon lokacinta, amma Magriba Mai riwayar ya manta abunda ya zo cikinta, kuma Nassoshi sun nuna haka Ijma'in Malamai kan cewa farkon lokacin ta da faduwar Rana, kuma Manzon Allah ya Kasance yana son ya jinkirta Isha, Saboda lokacinta wanda ya fi shi ne a Sallaceta a karshen lokacinta Na Mukhtari, kuma ya Kasance yana kin ayi Bacci kafinta don tsoron ya jinkirta ta daga lokacinta Mukhtari ko ya rasa Jam'i, da kuma tsoron bacci ya cimmasa da kuma barin Sallar dare kuma yana kin yin Hira bayanta saboda tsoron makara ga barin Sallar Asuba, ko rasa Sallar jam'i, Kamar yadda yana tafiya bayan Sallar Asuba, a lokacin da Mutum yana iya gane waye yake zaune a gefensa, tare da cewa zai Karanta a cikin sallarsa Aya Sittin zuwa dari, daga cikin abunda ya ke nuna cewa shi yana Sallatarta da duku duku.

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ. تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 24
Hadisai 24
  1. Yayin da mutane suke tsaye a sallar asuba yayin da suka zo, yana zuwa, sai ya ce: An saukar da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a gare shi a daren yau kuma an saukar da Alkur'ani, kuma an kira su su karbe shi, kuma sun karbe shi
  2. Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida, da Usama Dan Zaidu da Bilal da Usman Dan Dalha
  3. Ya Manzon Allah, Banyi Sallar La'asar ba har rana ta kusa faduwa, sai Annabi ya ce: "na rantse da Allah ban sallace ta ba, sai muka tashi zuwa Buthan, sai yayi Alwala don yin Sallah, Muma mukai Alwala don yin haka, sai mukai Sallah La'asar bayan rana ta fadi, sannan yai sallar Magariba bayan ta.
  4. Annabi tsira da amincin Allah ya kasance yana yin sallar Azahar a lokacin garjin rana, yakan sallaci La'asar lokaci da rana ta yi garau, Magariba kuma in rana ta fadi
  5. Ananbi tsira da amincin Allah ya yi dare bai fito sallar Issha'i ba, sai Umar ya fito yace: salla ya Manzon Allah mata da yara sun yi bacci, sai Manzo ya fito kansa yana digar da ruwa yana cewa: ba don kar in takurawa al'ummata ba, da na umarce su da yin wannan sallar a irin wannan lokacin.
  6. Manzon Allah tsira da amincin Allah ya kasance yana sallar Asuba, Muminai mata suna zuwa lullube da mayafansu, sannan su koma gidajensu ba wanda ke gane su, saboda sauran duhun dare.
  7. Na yi barci a hannun Manzon Allah - SAW- kuma kafafuna suna cikin sumbatansa, don haka lokacin da ya yi sujada, sai ya damke ni, sai kafafuna suka dafe
  8. Na shiga ni da Mahaifina ga Abu Baraza Al-aslami, sai Mahaifina ya ce da shi:yaya Annabi SAW yake sallar farilla?
  9. Kada xayanku ya kusura yayi Sallah da tufa xaya, babu komai a Kafaxunsa
  10. Jibrilu ya sauka, don haka na yi imani, don haka na yi salla tare da shi, sannan na yi salla tare da shi, sannan na yi salla tare da shi, sannan na yi salla tare da shi, sannan na yi salla tare da shi
  11. Lokacin yin sallar Zuhur idan rana ta wuce inuwar mutum in dai bai halarci Asuba ba, lokacin Asuba sai dai idan rana ta juye rawaya, lokacin sallar Magrib sai dai idan magariba ta yi sanyi, lokacin sallar magariba zuwa tsakar dare, da kuma lokacin sallar asuba daga fitowar alfijir sai dai idan rana ta fito.
  12. Sun zama masu kara zube; Ya fi girma ga ladanku, ko kuwa mafi girma ga ladanku
  13. Wanda ya riski raka'a daya ta safiya kafin rana ta fito to ya riga ya waye, kuma duk wanda ya riski raka'ar la'asar kafin rana ta fadi, to ya san zamani
  14. Ga alfijir na fitowar alfijir biyu: Amma alfijir wanda yake kamar zunubin Sarhan, salla ba ta halatta a cikin ta kuma ba a hana abinci.
  15. Allah baya karvar Sallar Wacce ta isa Haila sai da Hijabi
  16. Kada ɗayanku ya kuskura ya yi sallah da tufa ɗaya, babu komai a kafaɗunsa
  17. Munkasance tare da Manzon Allah SAW a wata tafiya a cikin dare mai duhu, bamu san ina ne Al-qibla ba, saboda haka sai kowane Mutum yayi Sallah zuwa gabansa, yayin da Muka wayi gari sai mu ka faxi hakan ga Manzon Allah SAW sai aka saukar da "To ko ina kuka fuskanta to nanne Fuskar Allah ta ke"
  18. Tsakanin Mafitar Rana da Mafaxarta akwai Al-qibla
  19. Manzon Allah SAW ya kasance yana Sallah akan abun Hawansa, ko ina tayi da shi idan kuma ya so yin Farillah ya sauka sai ya fuskanci Al-qibla
  20. Lallai Manzon Allah SAW ya kasance idan yayi tafiya sai ya so yin nafila sai ya kalli Al-qibla da Taguwarsa, sai yai Kabbara, sannan yayi sallah duk inda abunda abun hawansa yayi da shi
  21. Baki xayan Qasa Masallaci ce sai dai Maqabarta da kuma Banxaki
  22. Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu
  23. Idan aka kawo abincin dare, to kufara da shi kafin ku idar da faduwar rana, kuma kada ku yi sauri daga abincin dare
  24. An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com