Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini. Za’a gafarta masa zunubinsa

عَنْ سَعْدِ بْنِ أَبِي وَقَّاصٍ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ: «مَنْ قَالَ حِينَ يَسْمَعُ الْمُؤَذِّنَ أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، رَضِيتُ بِاللهِ رَبًّا وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، غُفِرَ لَهُ ذَنْبُهُ».
Daga sa'ad Dan Abu Wakkas - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini. Za’a gafarta masa zunubinsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah "Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya" wato: Ina tabbatarwa ina bada labarin cewa babu wani abin bautawa da agskiya sai Allah, kuma dukkan wani abin bauta wanda ba shi ba to shi karya ne, "Kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne" wato: shi bawa ne ba'a bauta masa, kuma Manzone ba ya karya, "Na yarda da Allah Shi ne Ubangiji" wato: Da RububiyyarSa da UluuhiyyarSa da sunayenSa da siffofinsa, "Da (Annabi) Muhammad shi ne Manzo" wato: Da dukkanin abinda aka aiko shi da shi, kuma ya isar da shi garemu, "Da Musulunci" wato: Da dukkanin hukunce-hukuncen Musulunci na umarni da hani, "Addini" wato: A kudircewa da aikatawa, "Za'a gafarta masa zunubinsa" wato: kananunsu.

Fa’idoji
  1. Maimaita wannan addu'ar a lokacin jin kiran sallah yana daga masu kankare zunubai.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 290) (386). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 39). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لملا علي القاري (2/ 562). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 254). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (2/ 771).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
KIRAN SALLAH DA IƘAMA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com