Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا سَمِعْتُمُ النِّدَاءَ، فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ المُؤَذِّنُ».
Daga Abu Sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwadaitarwa akan amsa wa ladani a lokacin jinsa, hakan da mu fadi irin abinda yake fada, jumla da jumla, A yayin da ya yi kabbara sai mu yi kabbara a bayansa, a yayin da ya zo da shaida biyu, sai mu zo da su a bayansa. An togance lafazin: (Ku yi gaggawa zuwa sallah, ku yi gaggawa zuwa tsira) cewa za'a fada a bayansu: Babu dabara babu karfi sai ga Allah.

Fa’idoji
  1. Zai bi ladani na biyu bayan karewar na farko, koda ladanan suna da yawa; dan gamewar hadisin.
  2. Ya amsawa ladani a kowanne hali, indai ba ya kasance ne a bayan gida ko yana kan biyan bukatarsa ba.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 126) (611). صحيح مسلم (1/ 288) (383). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص120). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 98).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
KIRAN SALLAH DA IƘAMA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com