Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya

عن قيس بن عاصم رضي الله عنه قال: أتيتُ النبيَّ صلى الله عليه وسلم أُريدُ الإسلامَ، فأَمَرَني أن أغتَسِلَ بماءٍ وسِدرٍ.
Daga Ƙais ɗan Asim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya.
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ƙais ɗan Asim ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali yana son ya musulunta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya yi wanka da ruwa da (ganyan) bishiyar magarya; don kasancewa ganyanta ana amfani da shi a tsafta; don kuma abin da take da shi na ƙamshi mai daɗi.

Fa’idoji
  1. Halaccin wankan kafiri a lokacin shigarsa Musulunci.
  2. Darajar Musulunci da kulawarsa da jiki da rai gabaɗaya.
  3. Cakuɗa ruwa da abubuwa masu tsarki ba ya fitar da shi daga tsarki.
  4. Abubuwa na tsafta na zamani suna tsayawa a matsayin magarya, kamar sabulu da makamantansa.
Madogara

سنن أبي داود (1/ 266) (355)، سنن الترمذي (1/ 595) (605)، سنن النسائي (1/ 109) (188)، معالم السنن (1/111)، ذخيرة العقبى (4/131)، شرح سنن أبي داود للعباد (54/ 10).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ABUBUWAN DA SUKE WAJABTA WANKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com

Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya · Hadisai tare da sharhi · Sabīl