Laƙiɗ Ibnu Sabira - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tare da waninsa daga mutanensa Banul Muntafiƙ, ya ce: Bamu same shi a gidansa ba, sai muka samu Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - sai ta yi umarni a yi mana farfesu na gari da romo, kuma aka kawo mana farantin da a cikinsa akwai dabino. Sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: Shin an kawo muku wani abu ne na abinci? Muka ce: Eh, Laƙiɗ ya ce: Muna zaune tare da shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ga mai kiwon tumakan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana korosu zuwa gurin kwanciyarsu, kuma yana ɗauke da jaririn ɗan bunsuru yana kuka, sai ya ce: Me aka haifa maka? Ya ce: Mace. Ya ce: To ka yanka mana wata akuyar babba a madadinta, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Kada ka yi zatan cewa mu saboda ku ne muka ɗorawa kanmu muka yanka muku ba, kawai mu muna da wasu tumakai ne guda ɗari, bama son adadin ya ƙaru akan wannan adadin, idan aka haifi sabon jinjiri sai mu yanka wani a madadinsa, Laƙiɗ ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa matata mai dogon harshe ce kuma mai alfasha ce, ya zan yi da ita? Ya ce: To ka saketa kawai. Ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah lallai tana tare da ni tuntuni, kuma akwai zuriya a tsakakninmu. Ya ce: To ka yi mata wa'azi, idan akwai alheri a tare da ita to zata ji wa'azinka, idan bata ji wa’azinba to ka daketa dukan da bazai sa rauni ba, kada ka daketa kamar yadda kake dukan bayinka. Sannan Laƙiɗ ya ce: Ya Manzon Allah, ka bani labari game da alwala. Ya ce: Ka isar da ruwa bigirensa a lokacin alwala, kuma ka cikawa kowace gaɓa haƙƙinta, kada ka bar wani abu daga cikin farillan alwala da sunnoninta, ka rarraba yatsun hannayenka da ƙafafuwanka a lokacin wanketa, kuma ka kai matuƙa a shaka ruwa a cikin hancinka a lokacin alwala da kuma fitar da shi saidai idan ka kasance ka ƙulla alwala dan kada ruwa ya shiga cikinka.
- Halaccin girmama baƙo.
- Cikawa nau'i biyu ne: 1. Cikawa ta wajibi, ita ce abinda alwala bata cika sai da shi, kuma ana nufin wanke bigiren da kuma game shi. 2. Cikawa ta mustahabbi, ita ce abinda alwala take cika ba tare da shi ba, kuma ana nufi da shi abinda ya ƙaru akan wajibi na wankewa ta biyu da na uku, to wannan mandubi ne.
- An so tsettsefe yatsun hannaye da ƙafafuwa a lokacin wanke su, kuma tsettsefe su shi ne sanya ruwan da zai kai tsakaninsu.
- Al-Ɗaibi ya ce: Kadai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa wasu daga cikin sunnonin alwala ne; domin cewa matambayin ya kasance ya san asalin alwala.
- Yana daga cikin kyawawan ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - himmatuwarsa kan abinda ke damun wasu da kuma lura da kansu.
- Hadisin dalili ne akan wajabcin kuskurar baki a cikin alwala,
- Hadisin dalili ne akan mustahabbancin kai matuƙa a cikin shaƙa ruwa sai dai ga mai azimi kawai to ba mustahabbi ba ne a cikin haƙƙinsa; dan kada kai matuƙar a cikin shaƙa ruwa ya kai zuwa shigar ruwa daga hanci zuwa maƙogwaro sai ya ɓata azimi.
- A cikinsa akwai dalili akan cewa hijira ba wajiba ba ce akan dukkan wanda ya musulunta; domin Banul Muntafiƙ da wasunsu ba su yi hijira ba, kawai sun aiko jama'arsu ne, shima kamar haka ne idan ya kasance yana gurin da yake da ikon bayyanar da Addininsa a cikinsa.
سنن أبي داود (1/ 99) (142). سنن الترمذي (2/ 146) (788). سنن النسائي (1/ 66) (87). سنن ابن ماجه (1/ 262) (407). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (1/ 217). سُبل السلام، للصنعاني (1/ 66 ). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 183). منحة العلَّام، لعبد الله الفوزان (1/ 174).