Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi, kuma ya ce: «Lallai su basa tsarkakewa».
Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya biya buƙatarsa na fitsari ne ko bahaya ya yi tsarkin hoge da ƙashin dabbobi ko torosonsa da busassun torosonsa; kuma ya ce: Lallai su basa kawar da najasa, kuma ba'a tsarkaka daga garesu.
Fa’idoji
Bayanin wasu daga cikin ladubban bayan gida da kuma tsarki.
Hani daga tsarkin hoge da toroson dabbobi; domin cewa shi: Kodai ya zama najasa, ko kuma domin cewa shi abincin dabbobin aljanu ne.
Hani akan yin tsarkin hoge da ƙashi; domin cewa shi kodai najasa ne, ko kuma domin abincin aljanu ne su da kansu.
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com