Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta (wasiku) zuwa ga Kisra, da Ƙaisara, da Najjashi, kai da dukkan mai tsaurin kai, yana kiransu zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -

عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ نَبِيَّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَتَبَ إِلَى كِسْرَى، وَإِلَى قَيْصَرَ، وَإِلَى النَّجَاشِيِّ، وَإِلَى كُلِّ جَبَّارٍ يَدْعُوهُمْ إِلَى اللهِ تَعَالَى، وَلَيْسَ بِالنَّجَاشِيِّ الَّذِي صَلَّى عَلَيْهِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta (wasiku) zuwa ga Kisra, da Ƙaisara, da Najjashi, kai da dukkan mai tsaurin kai, yana kiransu zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, amma ba Najjashin da Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sallah ba.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin rasuwarsa ya yi rubutu zuwa ga waɗanda ke kewaye da shi daga sarakunan al'ummu, yana kiransu zuwa ga Musulunci; sai ya rubuta zuwa ga Kisra, shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Farisawa, haka zuwa ga Ƙaisara shi kuma laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Rum, haka zuwa ga Najjashi shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Habasha. Kuma ya rubuta zuwa ga kowane sarki mai tsaurin kai wanda ya yi wa mutane tumbe, ya rinjaye su, kuma Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bayyana cewa Najjashin da aka rubuta masa ba Najjashin da ya musulunta ba ne kuma ya rasu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa sallah.

Fa’idoji
  1. Halaccin kiran waɗanda ba musulmai ba zuwa Musulunci, wanda ya haɗa manyan sarakunansu da kuma ƙananan sarakuna.
  2. Halaccin yin aiki da littafi da kuma wasiƙu.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1397) (1774). المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (3/ 612). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (31/ 67). النهاية في غريب الحديث والأثر (136).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
WASIƘUNSA DA SAƘONNINSA TSIRA DA AMINCIN SU TABBATA A GARESHI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com