Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Na tambayi Abdullahi Bin Amr game da mafi tsananin abunda Mushirikai ga Manzon Allah SAW sai ya ce: Naga Uqubuta Bin Abi Muaix Manzon Allah SAW kuma yana Sallah, sai ya sanya Mayafinsa a wuyansa sai ya shaqeshi shaqa mai tsanani

عن عُروة بن الزبير، قال: سألتُ عبد الله بن عمرو عن أشد ما صنع المشركون برسول الله صلى الله عليه وسلم ، قال: رأيتُ عُقبة بن أبي مُعَيْط جاء إلى النبي صلى الله عليه وسلم وهو يصلي، فوضع رداءه في عنقه فخنقه به خنقًا شديدًا، فجاء أبو بكر حتى دفعه عنه، فقال: {أَتَقْتُلُونَ رَجُلًا أَنْ يَقُولَ رَبِّيَ اللَّهُ وَقَدْ جَاءَكُمْ بِالْبَيِّنَاتِ مِنْ رَبِّكُمْ} [غافر: 28].
Daga urwa Bn Zubair ya ce: "Na tambayi Abdullahi Bin Amr game da mafi tsananin abunda Mushirikai ga Manzon Allah SAW sai ya ce: Naga Uqubuta Bin Abi Muaix Manzon Allah SAW kuma yana Sallah, sai ya sanya Mayafinsa a wuyansa sai ya shaqeshi shaqa mai tsanani, sai Abubakar ya zo har ya ture shi, sai ya ce: "Yanzu zaku kashe Mutum don yace Allah ne Ubangijinsa, kuma bayan ya zo muku da Ayoyi Mabayyana daga Ubangijinku" { Ghafir: 28)
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Urwa Bn Zubair ya ce: "Na tambayi Abdullahi Bin Amr game da mafi tsananin abunda Mushirikai ga Manzon Allah SAW sai ya ce: Naga Uqubuta Bin Abi Muaix Manzon Allah SAW kuma yana Sallah, sai ya sanya Mayafinsa a wuyansa sai ya shaqeshi shaqa mai tsanani, sai Abubakar ya zo har ya ture shi, sai ya ce: "Yanzu zaku kashe Mutum don yace Allah ne Ubangijinsa, kuma bayan ya zo muku da Ayoyi Mabayyana daga Ubangijinku" {Ghafir: 28) wannan ita ce shaidar mafi munin Abunda Abdullahi ya gani -Allah ya yarda da shi- kuma Urwa ya tsaya kan wannan shi ne ma tsananin abunda ya gani tunda Urwa ya bada labarin cewa Nana Aisha -Allah ya yarda da ita ta bashi labarin sa cewa ta ce da Manzon Allah SAW shi ka tava samun wata rana mafi tsanani a gareka kamar ranar Uhud? sai ya ce: "Na gamu abunda na gamu da shi daga Mutanenki kuma mafi tsananinsu ya kasance a ranar Aqaba lokacin da na gabatar da kaina ga Ibn Abd ya lail Bn Abd Kulal, bai amsa mun ba abunda na so, sai na tafi ina cikin vacin rai a fuskata, ban farka ba sai ina Qarn tha'alib sai na xaga kaina, sai ga girgije ya lulluveni, sai na duba sai Jibril a cikinsa, sai ya irani sai ya ce Allah yaji Maganar Mutanenka gareka, kuma da abunda suka mayar maka, haqiqa ya aiko Maka Mala'ika Duwatsu ka umarceshi da abunda ka so akan su, sai Mala'ikan Duwatsu ya kirani yayi mun Sallam sannan ya ce: ya Muhammad sai ya ce: Wancan sai abunda kaso in kaso in jeho shi akansu ? sai Manzon Allah SAW ya ce: aa ina son son a samu waxanda zasu futo daga ysatsonsu wanda zai bautawa shi kaxai, baya masa Shirka da komai" Buhari da Muslim suka rawaito shi

Madogara

صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه. عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لمحمود بن أحمد بن موسى الحنفى بدر الدين العينى، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري، لأحمد بن محمد بن أبى بكر بن عبد الملك القسطلاني القتيبي المصري، الناشر: المطبعة الكبرى الأميرية، مصر، الطبعة: السابعة، 1323 هـ. معجم اللغة العربية المعاصرة، للدكتور أحمد مختار عبد الحميد عمر بمساعدة فريق عمل، الناشر: عالم الكتب، الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZAMANIN (RAYUWAR) MAKKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com