Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur’ani kuma ya koyar da shi

عن عثمان رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «خَيْرُكُمْ مَنْ تَعَلَّمَ الْقُرْآنَ وَعَلَّمَهُ».
Daga Usman Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi ya ce: "Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur’ani kuma ya koyar da shi".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin mafi falalar Musulmai, wanda kuma yake ƙololuwar daraja a wurin Allah shi ne, wanda ya koyi Alƙur’ani, karatun da hadda da rerawa da fahimta da Tafsir. Ya kuma sanar da wani abin da yake wurinsa na iliman Alkur’ani (Ulumul Qur’an) tare da aiki da shi.

Fa’idoji
  1. Bayanin matsayin Alkur’ani, kuma shi ne mafificin zance; domin shi zancen Allah ne.
  2. Mafificin masu koyo shi ne wanda yake sanar da waninsa, ba wai wanda ya taƙaitu a kansa kawai ba.
  3. Koyon Alkur’ani da koyar da shi ya ƙunshi karatu da [sanin] ma’anoni da Hukunce Hukunce.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 192) (5027). فتح الباري شرح صحيح البخاري، لابن حجر العسقلاني (1/ 374). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 226). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخن وغيره (1/ 740). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 638).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR KULAWA DA ALƘUR'ANI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com