عن عُبَادَةَ بن الصَّامتِ رضي الله عنه قال: بَايَعْنَا رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم على السَّمْعِ وَالطَّاعَةِ فِي الْعُسْرِ وَالْيُسْرِ، وَالْمَنْشَطِ وَالْمَكْرَهِ، وعلى أَثَرَةٍ علينا، وعلى أَلَّا نُنَازِعَ الْأَمْرَ أهلَه، وعلى أَنْ نَقُولَ بِالْحَقِّ أينما كُنَّا، لا نَخَافُ في الله لَوْمَةَ لَائِمٍ.
Daga Ubada ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji da biyayya a halin rintsi da sauƙi, da farin ciki da baƙin ciki, da kuma nuna fifiko a kammu. Kuma kada mu yi wa ma'abota al'amari jayayya, kuma mu faɗi gaskiya a duk inda muke, ka da mu ji tsoron zargin mai zargi a al'amarin Allah.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya riƙi alƙawari daga sahabbansa wajen jagorantuwa (biyayya) ga majiɓinta al'amura da shugabanni a halin sauƙi da wahala, da halin wadata da talauci, kuma duk ɗaya ne umarninsu ya kasance daga abin da rai yake so ne ko yake ƙi, kai ko da shugabanni sun yi babakere da dukiyar jama'a ko muƙamai ko wanin hakan a kan talakawa; to, dole ne a ji [maganarsu] a yi biyayya bisa sanannun abubuwa, kada a yi musu tawaye, domin fitina da ɓarna wajen yaƙarsu ita ce mafi girma, kuma mafi tsanani daga ɓarnar da za ta faru saboda zaluncinsu, yana daga abin da suka yi alkawari a kansa cewa za su faɗi gaskiya a kowanne wuri suna masu yi wa Allah ikhlasi cikin haka, ba sa jin tsoron wanda zai zargesu.
Fa’idoji
- [Kyakkyawan] sakamakon ji da bi ga majiɓinta al'amura shi ne haɗuwar kan musulmai da watsar da rarrabuwa.
- Wajabcin ji da bi ga majiɓinta al'amura in ba a saɓon Allah ba ne a cikin sauƙi da tsanani, da farin ciki da baƙin ciki da babakeren da za su yi.
- Wajabcin faɗin gaskiya a duk inda muke, ba tare da mun ji tsoron zargin mai zargi ba cikin [al'amarin] Allah
Madogara
صحيح البخاري (9/ 47) (7055-7056)، (9/ 77) (7199، 7200).
صحيح مسلم (3/ 1470) (1709).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 277).
رياض الصالحين، للنووي (ص83) (186).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 419).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 202).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أُمِّ سَلَمَةَ أُمِّ المُؤمنين رضي الله عنها: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «سَتَكُونُ أُمَرَاءُ فَتَعْرِفُونَ وَتُنْكِرُونَ، فَمَنْ عَرَفَ بَرِئَ، وَمَنْ أَنْكَرَ سَلِمَ، وَلَكِنْ مَنْ رَضِيَ وَتَابَعَ» قَالُوا: أَفَلَا نُقَاتِلُهُمْ؟ قَالَ: «لَا، مَا صَلَّوْا».
Daga Ummu Salalmah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Za'a samu wasu shugabanni zaku sansu kuma zaku yi inkarinsu, wanda ya sani ya kubuta, wanda kuma ya yi inkari ya kubuta, saidai wanda ya yarda ya kuma bi" suka ce: Shin ba ma yakesu ba? ya ce: "A'a, muddin dai suna sallah".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa za'a shugabantar da wasu shugabanni akanmu, zamu san wasu daga ayyukansu; dan dacewarsu da abinda aka sani na shari'a, kuma zamu yi inkarin wasu ayyukan na su; dan sabawarsu ga hakan, Wanda ya ki da zuciyarsa amma ba shi da iko akan inkari; to hakika ya kubuta daga zunubi da kuma munafunci, Wanda ya samu iko akan inkari da hannu ko da harshe sai ya yi inkarin hakan akansu to hakika ya kubuta daga sabo da kuma tarayya a cikinsu, sai dai wanda ya yarda da aikinsu ya kuma bi su akansa zai halaka kamar yadda suka halaka.
Sannan suka tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Shin ba ba ma yaki shugabannin da wannan ita ce siffarsu ba? mu hanasu hakan, sai ya ce: A'a, muddin dai sun tsaida sallah a cikinku.
Fa’idoji
- Yana daga dalilan Annabcin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -yadda ya bada labari game da abinda zai auku na gaibu da kuma afkuwarsa kamar yadda ya bada labarin.
- Yarda da abin ki ba ya halatta ko tarayya a cikinsa, kuma inkarinsa yana wajaba.
- Idan shugabani suka farar da abinda ya sabawa shari'a to yi musu biyayya a kan hakan bai halatta ba.
- Rashin halaccin tawaye ga shugabannin musulmai; dan abinda yake biyo baya na barna da zubar da jini da rashin amincin akan hakan, to jurewar mai inkarin shugabanni, da hakuri akan cutar Warshu shi ne mafi sauki daga yi musu tawaye.
- Sallah al'amarinta mai girma ne, ita ce mai banbantawa tsakanin kafirci da musulunci.
Madogara
صحيح مسلم (3/ 1480) (1854).
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (4/ 64).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (32/ 206).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 279).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل بن عبد العزيز المبارك (ص150).
الشرح الممتع على زاد المستقنع، لابن عثيمين (11/ 323).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 435).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 211).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن الزبير بن عدي، قال: أَتَيْنَا أنسَ بنَ مَالِكٍ رضي الله عنه فَشَكَوْنَا إليه ما نَلْقَى من الحَجَّاجِ، فقال: «اصْبِرُوا، فإنه لا يأتي زمانٌ إلا والذي بعده شَرٌّ منه حَتَّى تَلْقَوا رَبَّكُم» سمعتُه من نَبِيِّكُم صلى الله عليه وسلم .
Daga Al-Zubayr bin Adi, ya ce: Mun zo wurin Anas bn Malik - Allah ya yarda da shi - kuma mun yi masa korafi game da abin da muka hadu da shi daga mahajjata, don haka ya ce: "Ka yi haƙuri, domin babu lokacin zuwa sai wanda na ji wani abu mara kyau daga bayansa".
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Al-Zubair bin Uday ya zo da wata tawaga zuwa wurin Anas bin Malik - Allah ya yarda da shi - bawan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - don su kai masa korafin abin da suka samu daga Al-Hajjaj bin Yusuf Al-Thaqafi, daya daga cikin sarakunan khalifofin Umayyawa, kuma ya kasance azzalumi mai taurin kai da aka san shi da zalunci da zubar da jini, don haka ya umarce su. Anas - Allah ya yarda da shi - tare da hakuri kan rashin adalci na shugabannin lamura, kuma ya gaya musu cewa babu wani lokaci da zai zo kan mutane face bayan hakan sun fi su sharri har sai sun hadu da Ubangijinsu, kuma ya ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Mugunta ba gabaɗaya ba ce kuma cikakkiyar mugunta ce, a'a tana iya zama mugunta a wasu wurare, kuma mai kyau a wasu.
Madogara
- دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، نشر دار الكتاب العربي.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407هـ - 1987م.
- شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426هـ.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي.
- صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال: «مَنْ خَرَجَ مِنَ الطَّاعَةِ، وَفَارَقَ الْجَمَاعَةَ فَمَاتَ، مَاتَ مِيتَةً جَاهِلِيَّةً، وَمَنْ قَاتَلَ تَحْتَ رَايَةٍ عِمِّيَّةٍ، يَغْضَبُ لِعَصَبَةٍ، أَوْ يَدْعُو إِلَى عَصَبَةٍ، أَوْ يَنْصُرُ عَصَبَةً، فَقُتِلَ، فَقِتْلَةٌ جَاهِلِيَّةٌ، وَمَنْ خَرَجَ عَلَى أُمَّتِي، يَضْرِبُ بَرَّهَا وَفَاجِرَهَا، وَلَا يَتَحَاشَى مِنْ مُؤْمِنِهَا، وَلَا يَفِي لِذِي عَهْدٍ عَهْدَهُ، فَلَيْسَ مِنِّي وَلَسْتُ مِنْهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuwar Jahiliyya, wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin makauniyar tuta, yana fushi saboda ƙabilanci, ko yake kira zuwa ƙabilanci, ko yake taimakon ƙabilanci, sai aka kashe shi, to, kisa ne na Jahiliyya, wanda ya yi fito na fito da al'ummata yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kiyaye wa tsakanin mumininta, kuma ba ya cika alkawari ga ma'abocin alkawari (kafirin amana), to, wannan ba ya tare da ni, ni ma ba na tare da shi".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya fita daga biyayyar majiɓinta al'amura, kuma ya rabu da jama'ar musulunci wacce ta haɗu a kan caffar (mubaya’a) shugaba, sai ya mutu a kan wannan halin na rabuwa da rashin biyayya, to, ya mutu irin mutuwar 'yan Jahiliyya, waɗanda ba sa bin wani shugaba, kuma ba sa tarowa zuwa jama'a ɗaya, kawai sun kasance ƙungiyoyi da jama'a-jama'a da sashinsu yana yaƙar sashi.
(Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin tutar da ba a fayyace gaskiyarta daga ƙaryarta ba, yana fushi saboda tsantsar ƙanilanci ga mutanensa ko ƙabilarsa, ba don taimakon Addini ko gaskiya ba, sai ya yi yaƙi don ƙabilanci ba tare da basira ko ilimi ba, to, idan aka kasheshi a kan wannan halin, ya zama kamar kisan Jahiliyya.
Kuma wanda ya yi fito na fito da al'ummarsa (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kulawa da abin da yake aikatawa kuma ba ya jin tsoron uƙubarsa na kashe mumininta, kuma ba ya cika alƙawari ga ma'abota alƙawari daga cikin kafirai ko majiɓinta al'amura sai dai ma yana warwaresu, to, wannan yana daga manyan zunubai, wanda ya aikata shi, to, haƙiƙa ya cancanci wannan narkon mai tsanani.
Fa’idoji
- Biyayya ga shugabanni wajiba ce a abinda ba saɓon Allah ba.
- A cikinsa akwai gargaɗi mai tsanani ga wanda ya fita daga biyayyar shugaba, kuma ya rabu da jama'ar musulmai, idan ya mutu a kan wannan halin, to, ya mutu a kan tafarkin ma'abota Jahiliyya.
- A cikin Hadisin akwai hani game da yaƙi don ƙabilanci.
- Wajabcin cika alƙawarurra.
- A cikin biyayya da lazimtar jama'a akwai alheri mai yawa, da aminci da nutsuwa, da gyara halaye.
- Hani daga kamanceceniya da halayen ma'abota Jahiliyya.
- Umarni da lazimtar jama'ar musulmai.
Madogara
صحيح مسلم.
شرح النووي على مسلم (12/ 238).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (6/ 179).
سبل السلام، لمحمد الصنعاني (2/ 374).
منحة العلام شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 338).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (6/ 2395).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عرفجة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ أَتَاكُمْ وَأَمْرُكُمْ جَمِيعٌ عَلَى رَجُلٍ وَاحِدٍ، يُرِيدُ أَنْ يَشُقَّ عَصَاكُمْ، أَوْ يُفَرِّقَ جَمَاعَتَكُمْ، فَاقْتُلُوهُ».
Daga Arfajah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya zo muku alhali al'amarinku gabaɗaya yana hannun mutum ɗaya (kanku a haɗe a ƙarƙashin shugabancin mutum ɗaya), kuma yana son ya tsaga sandarku, ko ya raba jama'arku, to, ku kashe shi ".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa musulmai idan suka haɗu a kan shugabancin mutum ɗaya, da jama'a ɗaya, sannan wani ya zo yana son ya yi jayayya da shi a shugabanci, ko yana son raba musulmai sama da kungiya ɗaya, to, ya wajaba su hana shi da kuma yaƙarsa; don tunkuɗe sharrinsa da kuma kare jinanen musulmai.
Fa’idoji
- Wajabcin ji da bi ga majinɓincin al'amarin musulmai in ba a saɓo ba, da haramcin yi masa tawaye.
- Wanda ya yi tawaye ga shugaban musulmai da jama'arsu, to, yaƙarsa tana wajaba duk yadda matsayinsa yake a daraja da nasaba.
- Kawaɗaitarwa a kan haɗa kai da rashin rabuwa da saɓani.
Madogara
صحيح مسلم (3/ 1480) (1852).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 349).
توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، للبسام (6/ 329).
فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 302).
المفاتيح في شرح المصابيح، الحسين المُظْهِري (4/ 295).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عُثْمَانَ الشَّحَّامِ، قَالَ: انْطَلَقْتُ أَنَا وَفَرْقَدٌ السَّبَخِيُّ إِلَى مُسْلِمِ بْنِ أَبِي بَكْرَةَ وَهُوَ فِي أَرْضِهِ، فَدَخَلْنَا عَلَيْهِ فَقُلْنَا: هَلْ سَمِعْتَ أَبَاكَ يُحَدِّثُ فِي الْفِتَنِ حَدِيثًا؟ قَالَ: نَعَمْ، سَمِعْتُ أَبَا بَكْرَةَ رضي الله عنه يُحَدِّثُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّهَا سَتَكُونُ فِتَنٌ، أَلَا ثُمَّ تَكُونُ فِتْنَةٌ الْقَاعِدُ فِيهَا خَيْرٌ مِنَ الْمَاشِي فِيهَا، وَالْمَاشِي فِيهَا خَيْرٌ مِنَ السَّاعِي إِلَيْهَا، أَلَا فَإِذَا نَزَلَتْ أَوْ وَقَعَتْ فَمَنْ كَانَ لَهُ إِبِلٌ فَلْيَلْحَقْ بِإِبِلِهِ، وَمَنْ كَانَتْ لَهُ غَنَمٌ فَلْيَلْحَقْ بِغَنَمِهِ، وَمَنْ كَانَتْ لَهُ أَرْضٌ فَلْيَلْحَقْ بِأَرْضِهِ»، قَالَ فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ أَرَأَيْتَ مَنْ لَمْ يَكُنْ لَهُ إِبِلٌ وَلَا غَنَمٌ وَلَا أَرْضٌ؟ قَالَ: «يَعْمِدُ إِلَى سَيْفِهِ فَيَدُقُّ عَلَى حَدِّهِ بِحَجَرٍ، ثُمَّ لِيَنْجُ إِنِ اسْتَطَاعَ النَّجَاءَ، اللهُمَّ هَلْ بَلَّغْتُ؟ اللهُمَّ هَلْ بَلَّغْتُ؟ اللهُمَّ هَلْ بَلَّغْتُ؟»، قَالَ: فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ أَرَأَيْتَ إِنْ أُكْرِهْتُ حَتَّى يُنْطَلَقَ بِي إِلَى أَحَدِ الصَّفَّيْنِ، أَوْ إِحْدَى الْفِئَتَيْنِ، فَضَرَبَنِي رَجُلٌ بِسَيْفِهِ، أَوْ يَجِيءُ سَهْمٌ فَيَقْتُلُنِي؟ قَالَ: «يَبُوءُ بِإِثْمِهِ وَإِثْمِكَ، وَيَكُونُ مِنْ أَصْحَابِ النَّارِ».
Daga Usman al-Shahhaam, ya ce: Ni da Farƙad al-Sabakhi mun tafi zuwa wurin Muslim ɗan Abu Bakrata alhali yana ƙasarsa, sai muka je wurinsa sai muka ce: Shin ka ji babanka yana zantarwa da wani hadisi a game da fitintinu? ya ce: Eh, na ji Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi - yana zantarwa, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai za'a samu wasu fitintinu, ku saurara sannan a samu wasu fitintinu wanda ke zaune a cikinsu ya fi wanda ke tafiya a cikinsu, mai tafiya ya fi wanda ke gaggawa zuwa garesu, ku saurara idan suka sauka ko suka faru wanda yake da raƙuma to ya riski raƙumansa, wanda yake da tumakai to ya riski tumakansa, wanda yake da wata ƙasa to ya risku da ƙasarsa», ya ce sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah to kana ganin wanda ba shi da raƙuma ko tumakai ko ƙasa fa? ya ce: «Ɗayanku ya nufi takobinsa sai ya caka tsinin takobin a dutse, sannan ya tsira idan zai iya tsira, ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar?». Ya ce: sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin idan aka tilastani har aka tafi da ni zuwa daya daga jama'a biyun, ko daya daga bangarori biyun, sai wani mutum ya dakeni da takobinsa, ko wata kibiya ta zo sai ta kasheni? ya ce: "Zai koma da zunubinsa da kuma zunubinka, kuma ya zama daga 'yan wuta".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Usman al-Shahham da Farƙad al-Sabakhi sun tambayi Muslim ɗan babban sahabi Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi -: Shin ya ji wani hadisi daga babansa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da fitintinu da yaƙin da zai afku tsakanin musulmai? sai ya ce: Eh, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa za'a samu wasu fitintinu bayan mutuwarsa, kuma waɗannan fitintinun wanda ke zaune babu ruwansa da su ya fi wanda ke tafiya a cikinsu alhali shi ba ya nemansu, yana bincike game da su, mai tafiya a cikinsu ya fi mai gaggawa zuwa garesu yana ta bincike game da su kuma yana tarayya a cikinsu. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da wanda fitina ta sauka ko ta faru a cikin zamaninsa kuma a wurinsa in ya samu wata mafakar da zai fake gare ta; wanda yake da raƙuman da yake kiwo to ya riski raƙumansa, wanda yake da tumakan da yake kiwo to ya riski tumakansa, wanda yake da wata ƙasa da gona to ya risku da ƙasarsa. Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin wanda ba shi da makoma fa na raƙuma ko tumakai ko ƙasa? Ya ce: Ya nufi makaminsa sai ya dandaƙa shi ya kamata shi, sannan ya gudu ya tsiratar da kansa da 'ya'yansa idan ya samu ikon tsira. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya shaidar sau uku sai ya ce: Ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar? Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin idan an tilastani in yi tarayya tare da ɗaya daga sahu biyun, ko ɗaya daga cikin jama'a biyun, sai wani mutum ya dakeni da takobinsa, ko wata kibiya ta zo ta kasheni fa? Ya ce: Zai koma da zunubin kansa da kuma zunubin wanda ya yi kisan, kuma ranar lahira ya zama daga 'yan wuta.
Fa’idoji
- Bada labarin faruwar fitintinu dan gargaɗarwa daga gareta, kuma mutane su yi musu tanadi, kada su kutsa cikinsu, kuma su roƙi Allah haƙuri da tsira daga sharrikansu.
- Nawawi ya ce; Faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Wanda ke a zaune ya fi wanda ke tsaye), har zuwa ƙarshensa, to ma'anarsa bayanin girman haɗarinsu, da kwaɗaitarwa akan nisantarsu, da guje musu, kuma cewa sharrinsu da fitinarsu zai zama akan gwargwadan rataya da su.
- Nawawi ya ce: An ɗauke zunubi ga wanda aka tilastawa akan halartar wurin, amma kisa ba'a halatta shi da tilastawa, kai wanda ya tilasta ɗin zai yi laifi akan wanda aka umarta da shi da ijma'in malamai.
- Ibnu Hajar ya ce: Wasu sun ce ; Idan wata ƙungiya ta yi wa shugaba tawaye sai ta hanu daga wajibin da ke kanta ta kuma kafa yaƙi to ya wajaba a yaƙeta, haka nan da ƙungiyoyi biyu zasu yi yaƙi to ya wajaba akan kowane mai iko ya riƙe hannun mai kuskuren da kuma taimakon wanda ke kan gaskiya, wannan ita ce maganar jumhur, wasu kuma suka rarrabe bayani, sai suka ce; Dukkan yaƙin da ya faru tsakanin ƙungiyoyi biyu daga musulmai inda babu wani shugaba ga jama'a to yaƙi a lokacin an hana, sai a saukar da hadisan da ke cikin wannan babin da waninsa akan haka.
- Nawawi ya ce: Haƙiƙa malamai sun yi saɓani a yaƙi lokacin fitina, sai wasu suka ce: Ba zai yi yaƙi ba a lokacin fitintinu tsakanin musulmai koda sun shiga gidansa, kuma sun nemi kashe shi, to ba ya halatta ya kare kansa; domin mai neman mai tawili ne, wannan ita ce mazahabar Abu Bakrata sahabi - Allah Ya yarda da shi - da waninsa, Ibnu Umar da Imran ɗan Hussain - Allah Ya yarda da su - da wasunsu suka ce: Ba zai shiga cikinta ba, sai dai idan ya yi nufin kare kansa, to waɗannan mazahabobi biyun sun haɗu akan barin shiga a dukkanin fitintinun Musulunci, mafi yawancin sahabbai da tabi'ai da gamewar maluman Musulunci suka ce: Ya wajaba a taimaki mai gaskiya a lokacin fitintinu, da tsayuwa tare da shi dan kashe 'yan tawaye kamar yadda Madaukakin sarki Ya ce: {To ku kashe wacce ta yi zalincin har sai ta koma zuwa umarnin Allah...} karanta ayar har karshenta, wannan shi ne ingantacce, kuma sun fassara hadisan akan wanda gaskiya ba ta bayyana gare shi ba, ko akan kungiyoyi biyun masu zalinci babu tawili ga wata daga cikinsu.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2212) (2887).
النهاية في غريب الحديث والأثر (91).
شرح سنن أبي داود للعباد (478/ 3).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com