عن أبي سعيد الخدري وأبي هريرة رضي الله عنهما مرفوعاً: "ما بعث الله من نبي ولا اسْتَخْلَفَ من خليفة إلا كانت له بطانتان: بطانة تأمره بالمعروف وتَحُضُّهُ عليه، وبطانة تأمره بالشر وتَحُضُّهُ عليه، والمعصوم من عصم الله".
Daga Abu Sa`id al-Khudri da Abu Hurairah - Allah ya yarda da su - tare da isnadi: “Allah bai aiko daga annabi ba, kuma ban sanya wanda zai gaje shi ba daga khalifa, amma yana da layi biyu: layin da yake umurtar shi da yi masa nasiha zuwa ga alheri, kuma layin da yake umartar shi da sharri da kwadaitarwa, kuma ma'asumi shine.
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي، الطبعة: الأولى 1418 هـ، 1997م.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة: الرابعة عشر، 1407هـ، 1987م.
رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، أبو زكريا محيي الدين النووي، تحقيق ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، الطبعة: الأولى 1428هـ، 2007م.
شرح رياض الصالحين، محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ مِنْ أَعْظَمِ الجِهَادِ كَلِمَةَ عَدْلٍ عِنْدَ سُلْطَانٍ جَائِرٍ».
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Yana daga mafi girman jihadi kalmar adalci a a gaban azzalumin sarki".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne da wani Sanadin
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga mafi girma da anfanin nau'ikan jihadi a tafarkin Allah - Madaukakin sarki - shi ne kalma ta adalci da gaskiya a wurin azzalumin sarki (shugaba); domin cewa shi aiki ne da alama ce ta horo da aikin alheri da hani daga mummuna, daidai ne ya kasance da fada ne ko rubutu ko aikatawa ko wanin hakan wanda maslaha zata tabbata da shi kuma barna ta tunkude barna.
Fa’idoji
- Horo da aikin alheri da hani daga mummuna yana cikin jihadi.
- Yi wa shugaba nasiha yana daga mafi girman jihadi, sai dai yana wajaba ya zama da ilimi da hikima da kuma tabbatarwa.
- AlKhaɗɗabi ya ce: Kaɗai hakan ya zama mafificin jihadi; domin wanda ya yaki makiyi ya kasance mai kaikawo tsakanin kwaɗayi da tsoro bai sani ba shin zai yi rinjaye ne ko za'a rinjaye shi, shi kuma mai yi wa shugaba nasiha abin rinjaya ne a hannunsa idan ya faɗi gaskiya kuma ya umarce shi da aikin alheri to hakika ya bijiro da salwantar da rayuwar sa, kuma ya kai kansa ga halaka, sai hakan ya zama mafificin nau’ukan jihadi saboda rinjayar da tsoro, an ce: Kaɗai hakan ya zama mafificin jihadi ne; domin shugaba da ya karbi maganarsa da anfanin ya game adadi mai yawa na mutane sai maslaha ta tabbata.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 45) (2174).
سنن أبي داود (6/ 400) (4344).
سنن ابن ماجه (5/ 144) (4011).
مسند أحمد (17/ 227) (11143).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 283).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 453).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 216).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَثَلُ القَائِمِ عَلَى حُدُودِ اللَّهِ وَالوَاقِعِ فِيهَا، كَمَثَلِ قَوْمٍ اسْتَهَمُوا عَلَى سَفِينَةٍ، فَأَصَابَ بَعْضُهُمْ أَعْلاَهَا وَبَعْضُهُمْ أَسْفَلَهَا، فَكَانَ الَّذِينَ فِي أَسْفَلِهَا إِذَا اسْتَقَوْا مِنَ المَاءِ مَرُّوا عَلَى مَنْ فَوْقَهُمْ، فَقَالُوا: لَوْ أَنَّا خَرَقْنَا فِي نَصِيبِنَا خَرْقًا وَلَمْ نُؤْذِ مَنْ فَوْقَنَا، فَإِنْ يَتْرُكُوهُمْ وَمَا أَرَادُوا هَلَكُوا جَمِيعًا، وَإِنْ أَخَذُوا عَلَى أَيْدِيهِمْ نَجَوْا، وَنَجَوْا جَمِيعًا».
Daga Nu'uman dan Bashir - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasansa sun kasance idan sun nemi ashayar da su ruwa sai sun wuce wadanda ke samansu, sai suka ce: Dama a ce zamu tsaga wata kafa a rabonmu ba mu cutar da wandanda ke samanmu ba, idan sun barsu da abinda suka yi nufi za su halaka gaba dayansu, idan suka yi riko da hannayensu za su tsira, sai su tsira gaba dayansu".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya buga misali ga tsayayyu akan dokokin Allah, masu tsayawa akan umarnin Allah, masu horo da aikin alheri, masu hani daga abin ki, da misalin masu afkawa dokokin Allah masu barin kyakkyawan aiki, masu aikata abin ki, da tasirin hakan a nasarar zamantakewar jama'a, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka hau jirgin ruwa, sai suka yi kuri'a ga wanda zai zauna a saman jirgin ruwan da wanda zai zauna a kasansa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasa idan sun so samun ruwa sai sun wuce ta wurin wadanda ke saman, sai wadanda ke kasa suka ce: Da a ce zamu tsaga wata tsaga a daidai wurin mu a kasa mu dinga samun ruwa daga gareshi, har ya zama bamu cutar da wanda ke samanmu ba, da a ce wadanda ke sama sun barsu su aikata hakan da jirgin ruwan ya nitse da su gaba daya, da a ce sun hanasu hakan da duk jama' biyun sun tsira.
Fa’idoji
- Muhimmancin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki a kiyaye zamantakewar jama'a da kuma tsiransu.
- Daga hanyoyin koyarwa akwai buga misalai, dan kusanto da ma'anoni ga hankula kamar ga abin.
- Aikata abin ki a zahiri tare da kin yin inkari akansa barna ce da zata cutar da kowa da kowa.
- Halakar jama'a tana kasance wa ne akan barin ma'abota barna suna barna a bayan kasa.
- Aiki na kuskure da kyakkyawan niyya ba sa isuwa a gyaruwar aiki.
- Nauyin aiki a cikin jama'ar musulmi na gaba daya ne, ba'a rataya shi ga wani ayyananan mutum.
- Azabtar da kowa da kowa saboda zunuban wasu mutane idan ba a yi hanani ba.
- Masu aikata mummunan aiki suna bayyanar da mummunan aikinsu mai makon su yi alheri ga jama'a kamar munafukai.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 139) (2493).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 277).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص149).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 430).
كنوز رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (4/ 39).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 210).
Wannan hadisi a HadeethEnc.com