Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HUKUNCIN UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA

Hadisai 3

Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da hannayensa ba, ya kusa Allah Ya gamesu da uƙuba daga gare shi

عَنْ أَبِي بَكْرٍ الصِّدِّيقِ رضي الله عنه أَنَّهُ قَالَ: أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّكُمْ تَقْرَؤُونَ هَذِهِ الآيَةَ: {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا عَلَيْكُمْ أَنْفُسَكُمْ لاَ يَضُرُّكُمْ مَنْ ضَلَّ إِذَا اهْتَدَيْتُمْ}، وَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِنَّ النَّاسَ إِذَا رَأَوْا الظَّالِمَ فَلَمْ يَأْخُذُوا عَلَى يَدَيْهِ أَوْشَكَ أَنْ يَعُمَّهُمُ اللَّهُ بِعِقَابٍ مِنْهُ».
Daga (Sayyidina) Abubakar Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: yaku mutane, lallai ku kuna karanta wannan ayar: {Yaku waɗanda suka yi imani ku lazimci kawunanku wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba idan kun shiriya}, lallai ni na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da hannayensa ba, ya kusa Allah Ya gamesu da uƙuba daga gare shi".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra da Ibnu Majah haka kuma AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi

(Sayyidina) Abubakar Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - yana bada labari: Cewa mutane suna karanta wannan ayar: {Yaku waɗanda suka yi imani ku lizimci kawunanku, wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba idan kun shiriya} [al-Ma'ida: 105]. Suna fahimta daga ayar cewa ya wajaba ga mutum ya yi ƙoƙari ya gyara kansa kawai, kuma ɓatan wanda ya ɓata ba zai cutar da shi ba bayan hakan, kuma su ba’a nema daga gare su su yi umarni da kyakkyawa kuma su hana mummuna ba. Sai ya sanar da su cewa ita ayar ba haka take ba, cewa shi ya ji annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai mutane idan suka ga azzalimi ba su hana shi zalincin ba, kuma suna da iko akan hana shin, ya kusa Allah Ya game su baki ɗaya da uƙuba daga gareShi, mai aikata abin ƙin, da mai yin shiru bai hana ba.

Fa’idoji
  1. Wajibin akan musulmai shi ne yin nasiha da horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi.
  2. Uƙubar Allah mai gamewa tana haɗo azzalimi dan zalincinsa, kuma tana haɗo mai yin shiru daga yin inkari, idan ya kasance mai iko ne akan yin inkarin.
  3. Sanar da bakiɗayan mutane da fahimtar da su nassosin AlKur'ani ta ingantacciyar fuska gare su.
  4. Yana wajaba akan mutum kula da fahimtar littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, dan kada ya fahimce shi ta hanyar da Allah - Maɗaukakin sarki - ba haka yake nufi ba.
  5. Shiriya ba ta tabbata tare da barin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi.
  6. Tafsirin daidai ga ayar: Ku lazimci kiyaye kawunanku daga saɓo, idan kun kiyaye kawunanku to ɓatan wanda ya ɓata ta hanyar aikata abubuwan da aka hana ba zai gajiyar daku ba, idan kun gajiya daga horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi, idan kun gane laifi kuma kun nisance shi.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 40) (2168). سنن أبي داود (6/ 393) (4338). السنن الكبرى للنسائي (10/ 88) (11092). سنن ابن ماجه (5/ 139) (4005). مسند أحمد (1/ 197) (16). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 286). كنوز رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (4/ 126). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 454). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 218).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani

عن أبي سعيد الخُدْريِّ رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «‌مَنْ ‌رَأَى ‌مِنْكُمْ ‌مُنْكَرًا فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الْإِيمَانِ».
Daga Abu Sa'id Al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin umarni da canza abin ki - wanda shi ne dukkanin abinda Allah da ManzonSa suka hana - gwargwadon iko, Idan ya ga wani abin ki to yana wajaba akansa ya canja shi da hannu idan yana da iko, Idan ya gajiya akan hakan, to ya canja shi da harshensa, ta hanyar hana mai aikatawar, kuma ya bayyana masa cutar hakan, ya kuma shiryar da shi zuwa alheri maimakon wannan sharrin, Idan ya gajiya daga wannan matakin, to ya canja shi da zuciyarsa shi ne ya ki wannan mummunan aikin, kuma ya yi niyyar cewa shi da yana da iko akan canja shi to da ya aikata, canzawa da zuciya shi ne mafi raunin matakan imani a canja abin ki.

Fa’idoji
  1. Hadisn asali ne a bayanin matakan canza abin ki.
  2. Umarni da bi sannu-sannu a hani ga abin ki, kowa gwargwadon iyawarsa da ikonsa.
  3. Hani daga abin ki wani babi ne mai girma a Addini kuma ba ya faduwa akan wani mutum, kuma ana dorawa kowanne musulmi shi gwargwadon ikonsa.
  4. Umarni da aikin alheri da hani daga abin ki yana daga dabi'un imani, kuma imani yana karuwa yana kuma raguwa.
  5. Ana sharadantawa a hani daga abin ki: Sanin cewa wannan aikin abin ki ne.
  6. Ana shardantawa a canja abin ki: Cewa kada wani abin kin mafi girma daga gare shi ya biyo baya.
  7. Akwai wasu ladubba da sharuddan da yake kamata ga musulmi ya sansu ga hani daga abin ki.
  8. Hani daga abin ki yana bukatuwa zuwa ga siyasa ta shari'a, kuma da ilimi da basira.
  9. Rashin inkari da zuciya yana nuni ga raunin imani.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 69). جامع العلوم والحكم (2/245). المعين على تفهم الأربعين (ص 393). شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 336). البحر المحيط الثجاج (2/204). فتح القوي المتين للعباد (ص 116).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

‌Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ: «لَا يَمْنَعَنَّ رَجُلًا مِنْكُمْ مَخَافَةُ النَّاسِ أَنْ يَتَكَلَّمَ بِالْحَقِّ إِذَا رَآهُ أَوْ عَلِمَهُ».
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa».
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa huɗuba, daga cikin abinda ya yi musu wasicci da shi cewa kada tsoro da kwarjinin mutane da kuma ƙarfinsu ya hana musulmi faɗin gaskiya ko umarni da ita idan ya ganta ko ya santa.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan bayyanar da gaskiya da kuma rashin ɓoyeta dan jin tsoron mutane.
  2. Faɗin gaskiya ba ya nufin rashin lazimtar ladabi ta hanyar faɗinta da kuma hikima da kyakkyawan wa'azi a cikinta.
  3. Wajabcin inkarin munkari, da kuma gabatar da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - akan mas'lahohin mutane waɗanda sukaci karo da ita.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 53) (2191). سنن ابن ماجه (5/ 141) (4007). مسند أحمد (17/ 490) (11403).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com