Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alhali shi yana algus ga abin kiwonsa sai Allah Ya haramta masa aljanna

عن مَعقِلِ بن يَسار المُزَنِيّ رضي الله عنه قال: إني سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «مَا مِنْ عَبْدٍ يَسْتَرْعِيهِ اللهُ رَعِيَّةً، يَمُوتُ يَوْمَ يَمُوتُ وَهُوَ غَاشٌّ لِرَعِيَّتِهِ، إِلَّا حَرَّمَ اللهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ».
Daga Ma'aƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alhali shi yana algus ga abin kiwonsa sai Allah Ya haramta masa aljanna".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ba da labarin cewa kowane mutumin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanyashi majiɓinci, kuma shugaba ga mutane, duk ɗaya ne ya kasance shugabanci ne mai gamewa kamar sarki, ko keɓantaccen shugabanci ne kamar mutum a gidansa da mace a gidanta, sai ya gaza a haƙƙin waɗanda aka ba shi kiwonsu, ya yi musu algus bai yi musu nasiha ba, sai ya tozarta haƙƙoƙinsu na addini da na duniya, to, haƙiƙa ya cancanci wannan uƙubar mai tsanani.

Fa’idoji
  1. Wannan narkon bai keɓanci babban shugaba ba da mataimakansa, kai, shi mai gamewa ne a dukkanin wanda Allah Ya ba shi kiwon wani abin kiwo.
  2. Wajibi a kan dukkanin wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin musulmai ya yi musu nasiha, kuma ya yi ƙoƙari wajen ba da amana, kuma ya kiyayi ha'inci.
  3. Girman nauyin da ke wuyan dukkanin wanda ya jiɓinci wani abin kiwo mai gamewa, ko keɓantacce, babba ne ko ƙarami ne.
Madogara

صحيح البخاري (9/ 64) (7150). صحيح مسلم (1/ 125) (142). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 706). فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (5/ 488). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 543).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIYASA A SHARI'ANCE

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com