Daga Mus'ab ɗan Sa'ad ya ce: Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ga cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ana taimakonku ne ko ana azurtaku sai saboda raunananku".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya yi zatan cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi daga raunana saboda gwarzantakarsa da makamancin haka! Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Shin ana taimakonku ne kuma ana azirtaku ai sai saboda raunananku ta hanyar addu'o'insu da sallalolinsu da ikhlasinsu; domin su a galibi su ne mafi tsananin ikhlasi a cikin addu'a, kuma mafi yawan khushu'i a cikin ibada dan wofintar zuciyarsu daga rataya da ƙawace-ƙawacen duniya.
Fa’idoji
Kwaɗaitarwa akan tawali'u da hana rena wasu daban.
Ibnu Hajar ya ce: Idan mai ƙArgo yana rinjaya saboda gwarzantakara, to shi mai rauni yana rinjaya saboda falalar addu'arsa da kuma ikhlasinsa.
Kwaɗaitarwa akan kyautatawa talakawa da basu haƙƙoƙinsu, domin hakan yana daga sabubban rahamar Allah gareka da kuma taimakonSa.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 36) (2896).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 354).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 111).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 279).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com