Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi zuwa aikin da idan ya aikata shi Allah zai so shi kuma mutane ma zasu so shi, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Allah zai so ka idan ka bar mafifici a duniya, da abin da ba zai amfaneka a lahira ba, kuma ka bar abin da zai iya yi wuwa a cikinsa akwai cutarwa a Addinika, kuma mutane zasu so ka idan ka guji abinda ke hannunsu na duniya; domin su a ɗabi'arsu suna sonta, wanda kuwa ya yi gogayya da su a kanta zasuƙi shi, wanda ya bar musu ita zasu so shi.
- Falalar gujewa duniya, shi ne: Yabar abin da ba zai amfanar a lahira ba.
- Gudun duniya darajarsa ta fi tsantseni; domin cewa tsantseni shi ne barin abin da zai iya cutarwa, gudun duniya kuwa shi ne barin abin da ba zai amfanar a lahira ba.
- Sindi ya ce: Lallai cewa duniya abar so ce a wurin mutane, duk wanda ya yi gogayya da su a cikinta zai zama abin ƙi a wurinsu gwargwadan haka, wanda kuma ya barsu da abar sonsu zai zama abin so a cikin zukatansu gwargwadan hakan.
الأربعون النووية (ص118) (ح31). سنن ابن ماجه (5/ 225) (4102). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص73). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين (ص111). الفوائد المستنبطة من الأربعين النووية، للشيخ عبد الرحمن البراك (ص87). الأحاديث الأربعون النووية وعليها الشرح الموجز المفيد، لعبد الله بن صالح المحسن (1/61).