Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَنَّهُ كَانَ يَقُولُ إِذَا أَصْبَحَ: «اللهُمَّ بِكَ أَصْبَحْنَا، وَبِكَ أَمْسَيْنَا، وَبِكَ نَحْيَا، وَبِكَ نَمُوتُ، وَإِلَيْكَ النُّشُورُ» وَإِذَا أَمْسَى قَالَ: «بِكَ أَمْسَيْنَا، وَبِكَ أَصْبَحْنَا، وَبِكَ نَحْيَا، وَبِكَ نَمُوتُ، وَإِلَيْكَ النُّشُورُ» قَالَ: وَمَرَّةً أُخْرَى: «وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Cewa shi ya kasance idan ya wayi gari yana cewa: "Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa" Idan ya shiga maraice ya ce: "Da (kiyayewarka) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (al'amarin) Ka zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gare Ka" ya ce: Wani lokaci kuma: "Makoma tana gare Ka".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin Alkubra da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance idan ya wayi gari shi ne farkon yini tare da ɓullowar alfijir yana cewa: (Ya Allah da (kiyewar) Ka ne muka wayi gari) muna masu cakuɗuwa da kiyayewarKa ababen lulluɓewa da ni'imominKa, masu shagaltuwa da ambatanKa, masu neman taimako da sunanKa, masu tarowa da dacewarKa, masu motsawa da dabararKa da kuma ƙarfinKa, (da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (kiyayewar) Ka ne muka rayu, da (kiayewar) Ka ne zamu mutu) wato kamar lafazin da ya gabata tare da sanya shi a sama, sai ya ce: Ya Allah da Kai ne muka shiga maraice, kuma da sunanKa ne Mai rayawa muke rayuwa, da sunaKa ne Mai kashewa zamu mutu, (kuma gareKa ne tashi yake) da tashi bayan mutuwa, da rarrabuwa bayan haduwa, halinmu zai ci gaba akan haka a cikin dukkan lokuta, da ragowar halaye ba zan rabu ba daga gare shi kuma ba zan kaurace masa ba. Idan ya shiga maraice bayan la'asar ya ce: "Ya Allah da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (umarnin) Ka ne muke rayuwa, kuma (da al'amarin) Ka ne zamu mutu, makoma tana gare Ka) makoma a duniya, da makoma a ƙarshe, Kaine Kake rayani kuma kaine zaKa kasheni.

Fa’idoji
  1. An so wannan addu'ar safe da yamma, dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  2. Buƙatuwar bawa ga Ubangijinsa a cikin dukkan halayensa da lokutansa.
  3. Abin da yafi a karanta zikirai, a safiya: Daga ɓollowar alfijir zuwa ɓullowar rana a farkon yini, haka kuma daga bayan la'asar zuwa kafin faɗuwar rana, idan ya faɗesu bayan hakan yana nufin: -Ya faɗesu a safiya bayan ɗagawar walaha - ya isar masa, idan ya faɗesu bayan azahar ya isar masa, idan ya faɗesu bayan Magariba ya isar masa, to wannan lokaci ne na zikiri.
  4. Munasabar faɗinsa: " Tashi yana gare Ka" da safe, wannan yana tunatar da shi da rayuwa da tashi babba lokacin da mutane zasu mutu kuma a tashesu ranar alƙiyama, to wannan tashine sabo, kuma yini ne sabo da ake dawo da rayuka a cikinsa, kuma mutane suke watsuwa a cikinsa, wannan sabuwar safiyar wacce Allah Ya halicceta zata nunfasa; dan ta zama mai shaida akan ɗan Adam, kuma lokutansa da sakwankwaninsa su zama taskar ayyukansa.
  5. Munasabar faɗinsa: "Makoma tana gareKa" da yamma, lokacin da mutane suke dawowa daga ayyukansu da watsuwarsu a abubuwan maslahohinsu da rayuwarsu, zasu dawo zuwa gidajensu, zasu dawo zuwa hutu bayan sun rarrabu, sai ya tuna makoma da komawa zuwa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -
Madogara

سنن أبي داود (7/ 404) (5068). سنن الترمذي (5/ 398) (3391). السنن الكبرى للنسائي (9/ 209) (10323). سنن ابن ماجه (5/ 35) (3868). مسند أحمد (14/ 290) (8649). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 576). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 458). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 503). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، لمحمد الصنعاني (2/ 714).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZIKIRAN SAFIYA DA YAMMA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com