Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «البَسُوا مِنْ ثِيَابِكُمُ البَيَاضَ، فَإِنَّهَا مِنْ خَيْرِ ثِيَابِكُمْ، وَكَفِّنُوا فِيهَا مَوْتَاكُمْ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana shiryar da maza cewa su sa tafafi masu farin launi da kuma yi wa mamata likkafani a cikinsu; domin cewa sune mafi alherin tufafi.

Fa’idoji
  1. An so sanya farin tufafi, kuma waninsa na wata kalar ma yana halatta.
  2. An so yi wa mamata likkafani da fararen (tufafi).
  3. Shaukani ya ce: Hadisin yana nuni akan halaccin sanya fari da yi wa mamata likkafani da shi; kasancewarsa ya fi waninsa tsarkaka, amma kasancewarsa ya fi tsarki to wannan zahiri ne, amma kasancewarsa ya fi tsafta domin cewa mafi ƙanƙatar abu idan ya faɗa kansa zai bayyana sai ya fifita.
Madogara

سنن أبي داود (6/ 27) (3878). سنن الترمذي (2/ 311) (994). سنن ابن ماجه (2/ 453) (1472). ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (19/ 16).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN TUFAFI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com