عَنْ عُمَرَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ لَبِسَ الحَرِيرَ فِي الدُّنْيَا لَمْ يَلْبَسْهُ فِي الآخِرَةِ».
Daga Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya sanya alhariri a duniya ba zai sanya shi a lahira ba"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya sanya alhariri cikin maza a nan duniya ba zai sanya shi a lahira ba idan bai tubaba dan ukuba gare shi.
Fa’idoji
- Abin nufi da alhariri shi ne tataccen alhariri na dabi'a, amma alhariri na sana'antawa to Hadisin bai kunshe shi ba.
- Haramcin sanya alhariri ga maza.
- Hanin sanya alhariri ya game sanya shi da kuma shinfida shi.
- An yi rangwame ga maza su sanya wani abu na alhariri a tufa da abinda bai ketare yatsu biyu zuwa yatsu hudu da za'a a yi alamomi ko ragowar tufa ba.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 150) (5834). صحيح مسلم (3/ 1641) (2069). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (4/ 207).