Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ba ya ƙin karɓar turare

عن أنس بن مالك رضي الله عنه: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ لَا يَرُدُّ الطِّيبَ.
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ba ya ƙin karɓar turare.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ya kasance daga cikin karantarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ya ƙin karɓar turare, yana karɓarsa domin yana da sauƙin ɗauka, kuma yana da ƙamshi.

Fa’idoji
  1. Mustahabbacin karɓar kyautar turare, domin babu wata wahala wurin ɗaukarsa, babu damuwa wurin karɓarshi
  2. Cika da kyakkyawan halin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wurin ƙin karɓar turare da kuma karɓar kyauta daga wanda ya yi masa.
  3. Kwaɗaitarwa a kan amfani da turare.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 157) (2582). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 560). منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، لحمزة قاسم (4/ 9). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخن وغيره (2/ 1213).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN ZIYARA DA NA NEMAN IZINI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com