Daga Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya yalwaceka, ka yi kuka akan kuskurenka".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sabubban tsirar mumini a duniya da lahira?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Na horeka da al'amura uku:
Na farko: Ka kiyaye harshenka daga abinda babu alheri a cikinsa, daga faɗar kowane sharri, kuma kada ka yi wani furuci sai da alheri.
Na biyu: Ka lazimci gidanka dan ka bautawa Allah a cikin kaɗaitakarka, ka shagalta da biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, ka nisanci fitinu a cikin gidanka.
Na uku: Ka yi kuka ka yi nadama ka tuba daga abinda ka aikata na zunubai.
Fa’idoji
Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan sanin hanyoyin tsira.
Bayanin sabubban tsira a duniya da lahira.
Kwaɗaitarwa akan shagaltar mutum da kansa idan ya gajiya daga anfanar waninsa, ko ya ji tsoron cutarwa akan Addininsa da kansa idan ya cakuɗa da mutane.
Nuni zuwa himmatuwa da gida musamman ma dai a lokacin fitintinu, shi yana daga hanyoyi dan kiyaye Addini.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 208) (2406).
مسند أحمد (28/ 654) (17452).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (3/ 15).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1039).
مرقاة المفاتيح، لعلي القاري (7/ 3039).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com