Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku

عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: لَمْ يَكُنِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَاحِشًا وَلَا مُتَفَحِّشًا، وَكَانَ يَقُولُ: «إِنَّ مِنْ خِيَارِكُمْ أَحْسَنَكُمْ أَخْلَاقًا».
Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa kasance wa mai alfasha ba, ko mai ƙoƙarin alfasha ba, ya kasance yana cewa: Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Mummunar magana ko mummunan aiki ba su kasance cikin dabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba, bai nufe shi ba, kuma bai ganganta yinsa ba, to, shi fa [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ma’abocin ɗabi’u ne masu girma. Kuma [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa: Lalle mafi falalarku a wurin Allah mafi kyawunku kyawawan ɗabi’u, ta hanyar bayar da abu mai kyau, da sakin fuska, da kamewa daga cutarwa, da juriya, da hulɗa da mutane da abu mai kyau.

Fa’idoji
  1. Ya wajaba ga mumini ya yi nesa da mummunar magana da kuma mummunan aiki.
  2. Cikar ɗabi’un Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ba abin da yake zuwa daga gare shi sai kyakkyawan aiki da daddaɗan zance.
  3. Kyawawan ɗabi’u wani fage ne da ake rige - rige, duk wanda ya Riga, ya kasance zababbe cikin muminai kuma mafi cikar imaninsu.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 189) (3559). صحيح مسلم (4/ 1810) (2321). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 672). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص410).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com