Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lalle sassauci ba ya kasance wa a komai sai ya ƙara masa kyau, kuma ba a cire shi a komai sai ya aibanta shi

عن عائشة رضي الله عنها زوج النبي صلى الله عليه وسلم عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «إِنَّ الرِّفْقَ لَا يَكُونُ فِي شَيْءٍ إِلَّا زَانَهُ، وَلَا يُنْزَعُ مِنْ شَيْءٍ إِلَّا شَانَهُ».
Daga Nana Aisha Allah Ya yarda da ita, matar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta ta ce: Lalle sassauci ba ya kasance wa a komai sai ya ƙara masa kyau, kuma ba a cire shi a komai sai ya aibanta shi.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewa rangwame da sauƙi da bi-sannu - sannu a magana da aiki suna ƙarawa abu kyau da cika da ƙaye, kuma nan ne ya fi cancanta mutum ya samu buƙatarsa. Rashin sassauci yana aibanta lamura yana muzanta su, kuma yana hana mai hakan cimma buƙatarsa, in kuma ya samu, to, da baƙar wahala ne.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan ɗabi’antuwa da halin sauƙaƙawa.
  2. Sauƙaƙawa tana ƙawata mutum, ita ce dalili na alheran duniya da lahira.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2004) (2594). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 683). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص414).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com