Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa

عن سعد بن أبي وقاص رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إِنَّ اللهَ يُحِبُّ الْعَبْدَ التَّقِيَّ الْغَنِيَّ الْخَفِيَّ».
Daga Sa’ad Ɗan Abu Waƙƙas, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa Allah mabuwayi Yana son wasu daga cikin bayinsa. Daga cikinsu akwai: Mai tsoron Allah wanda yake aikata abin da aka yi umarni, yake kuma nisantar hani. Kuma yana son: Wanda ya wadatu ga barin mutane, ya yi riƙo da Allah maɗaukaki, ba ya waigawa ga wanin Allah. Kuma yana son: Mai ɓoye kansa (wanda ba ya neman suna), mai tawalu’u, mai bauta ga Ubangijinsa, wanda ya shagaltu da abin da zai amfane shi, wanda bai damu da wani ya sanshi ba, ko wani ya yabe shi ba, ko ya burge ba.

Fa’idoji
  1. Bayanin wasu siffofi masu sanyawa a samu son Allah ga bayinsa, wadanda suke su ne, Taƙ'wa da Tawalu’u da kuma yarda da abin da Allah ya raba.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2277) (2965). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 651). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 509). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 509). شرح النووي على مسلم (18/ 100).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com